Allah Ya yi wa Sarkin Gazargamu rasuwa

Alhaji Ahmad Tijjani Ibn Saleh, rasuwa ya rasu ne a Kasar Masar sakamakon doguwar jinya

Allah Ya yi wa Sarkin Gazargamu rasuwa

Alhaji Ahmad Tijjani Ibn Saleh

A yau Talata ne Allah Ya yi wa Mai Martaba Sarkin Gazargamu da ke Jihar Yobe, Alhaji Ahmad Tijjani Ibn Saleh, rasuwa.

Dan marigayin, Injiniya Tijjani Hamisu Bala, wanda shi ne Janar-Manaja na Hukumar Kula da Sufuri ta Jihar Yobe, ne ya tabbatar da rasuwar.

Ya bayyana cewa, Marigayi Alhaji Ahmad Tijjani Ibn Saleh, rasuwa ya rasu ne a Kasar Masar inda ya yi doguwar jinya.

Zuwa lokacin da muka kammala wannan rahoton babu wani bayani game da shirye-shiryen jana’izar basaraken.