An ceto ’yar shekara 2 da maƙocinsu ya sace ta a Kano

An ruwaito cewar ya nemi Naira miliyan biyu a matsayin kuɗin fansa.

An ceto ’yar shekara 2 da maƙocinsu ya sace ta a Kano

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, ta ceto wata yarinya ‘yar shekara biyu mai suna Amina da wani maƙocinsu, Zakariyya Muhammad, ya sace ta a unguwar Sabuwar Ganduje da ke jihar.

Maƙocin ya nemi kuɗin fansa Naira miliyan biyu kafin ya sako yarinyar.

Wata sanarwa da kakakin rundunar ’yan sandan jihar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya sanya wa hannu, ta ce wani mazaunin Sabuwar Gandu Kwarin Barka ne ya sanar da faruwar lamarin.

Kwamishinan ’yan sandan jihar, Salman Dogo Garba, ya tura tawagar yaƙi da garkuwa da mutane, inda suka kama wanda ake zargin cikin sa’o’i 24.

Rundunar ’yan sandan ta ce jami’an leƙen asirin sun yi nasarar cafke wanda ake zargin mai Zakariyya Muhammad, mai shekara 22 wanda mazaunin Sabuwar Gandu Kwarin Barka ne.

Sanarwar ta ce matashin ya amsa aikata laifin shi kaɗai, sannan ya jagoranci ’yan sanda zuwa inda ya ɓoye yarinyar.

An ceto Amina sannan an garzaya da ita asibitin ƙwararru na Murtala Muhammed da ke Kano, inda aka duba lafiyarta, sannan aka sallame ta.

Kwamishinan ’yan sandan jihar, ya yi kira da mazauna jihar da su kai rahoto ga ‘yan sanda a duk lokacin da suka zargi wani abu na tafiya ba daidai ba.

Firimiya: Manchester United da Chelsea sun yi kunnen doki

Tinubu zai rantsar da sabbin ministoci a ranar Litinin

Da ni ne mulki a Najeriya da ba ta shiga tasku ba — Atiku

Bayan hukuncin CAF an fara kamen ’yan Najeriya a Libya