An fara shirye-shiryen tsige mataimakin shugaban ƙasar Kenya

Ana zargin mataimakin da goyon bayan zanga-zangar adawa da gwamnatin shugaba William Ruto.

An fara shirye-shiryen tsige mataimakin shugaban ƙasar Kenya

Wasu ’Yan Majalisun Dokokin Ƙasar Kenya, sun gabatar da ƙudiri domin tsige mataimakin shugaban ƙasar, Rigathi Gachagua kan zargin sa da saɓa wa kundin tsarin mulkin ƙasar.

Wanda dai ka zuwa ne bayan alaƙa ta fara tsami tsakaninsa da shugaba William Ruto.

Shugaban Majalisar Dokokin ƙasar, Moses Wetang’ula, ya ce sama da kashi ɗaya bisa uku na ‘yan majalisun sun rattaba hannu kan buƙatar tsige mataimakin shugaban ƙasar.

Wannan ƙudiri ya samu ne bayan wani ɗan majalisa Mwengi Mutuse, wanda yake na hannun damar Ruto, ya gabatar.

Daga cikin ƙorafin da ake yi a kan mataimakin shugaban ƙasar sun haɗa hana bai wa jama’ar ƙasar damar samun gurabun ayyukan gwamnati da kuma raba dukiyar ƙasa tare da goyon bayan zanga-zangar adawa da gwamnatin shugaba Ruto.

Taƙaddama tsakanin shugaba Ruto da mataimakinsa Gachagua, ta fito fili a ‘yan kwanakin nan, lamarin da ya sanya mataimakin bayyana ɓacin ransa dangane da yadda aka mayar da shi saniyar ware wajen gudanar da mulki.

Yayin da ya nesanta kansa da magoya bayansa daga zanga-zangar adawa da gwamnatin da aka yi a farkon wannan shekarar.

Wannan shi ne karo na farko da za a gwada amfani da kundin tsarin mulkin da aka samar a shekarar 2010 wajen tsige mataimakin shugaban ƙasa daga muƙaminsa.