An kama matar auren da ta kitsa garkuwa da kanta a Delta

Wannan lamarin ya yi matuƙar girgiza ’yan uwannu, musamman ganin cewa mahaifinmu yana fama da rashin lafiya.

An kama matar auren da ta kitsa garkuwa da kanta a Delta

Jihar Delta

An kama wata matar aure mai suna Oluchi, wadda ta kitsa garkuwa da kanta domin karɓar kuɗin fansa a wurin ’yan uwanta.

Aminiya ta ruwaito cewa an dai gano matar ce tare da wani mutum da ake zargin saurayinta ne a ɗakin wani otel da ke Jihar Delta.

Wannan dai na zuwa ne bayan da ’yan uwa da abokan arziki suka fara tara gudunmawar kuɗin fansa domin ceto ta, yayin da ta bayyana a gare su cewa waɗanda suka yi garkuwa da ita suna nema a biya su Naira miliyan 50 a matsayin kuɗin fansa, amma daga bisani suka yi rangwami zuwa Naira miliyan 20.

Tun da farko dai ’yan uwan Oluchi sun kai wa ’yan sanda rahoton cewa an sace ta ne a yankin Ikpoba Hill da ke Ƙaramar Hukumar Ikpoba-Okha a Jihar Edo.

’Ya’yanta, ciki har da wata ’yarta mai zama a ƙasar Canada mai suna Anita, sun yi kira ga jama’a da su taimaka wajen tara kuɗin fansar domin ceto mahaifiyarsu.

Sai dai binciken da ’yan sanda suka gudanar ya kai su wani otel da ke Ubiaroko a Jihar Delta, inda suka gano matar tare da wani mutum.

Wata majiya da ke da masaniya kan binciken ta shaida wa jaridar Punch cewa jami’an tsaro sun bi sawun wata lambar waya da ake zargin tana da alaƙa da ɗaya daga cikin waɗanda ake bincika.

“’Yan sanda sun gano inda mutumin yake ta hanyar bin sawun lambarsa zuwa wani otel da ke Ubiaroko a Jihar Delta. A can suka tarar da shi tare da matar da aka ce an yi garkuwa da ita,” in ji majiyar.

Bayan gano hakan, an sanar da mijin matar halin da ake ciki.

Da take mayar da martani a wani bidiyo da ya yaɗu a kafafen sada zumunta, Anita ta bayyana matuƙar kaɗuwarta da sakamakon binciken.

“An sako mahaifiyata, amma an gaya mana cewa tana da hannu a lamarin. Duk abin da na yi, na yi ne domin ceton rayuwarta,” in ji ta.

Ta ce tun farko iyalansu sun haɗa kai da jami’an tsaro wajen binciken lamarin, amma ba su biya ko sisin kwabo a matsayin kuɗin fansa ba.

“An kira mu aka sanar da mu cewa an sako mahaifiyata. Ba mu biya kuɗin fansa ba, kuɗin da aka tara yana nan kuma za mu mayar da shi. Tun farko mun sanar da ’yan sanda, yanzu mun gano cewa ba garkuwa ba ce ta gaskiya,” in ji ta.

Anita ta kuma yi zargin cewa masu bincike sun gaya musu cewa mahaifiyarta da mutumin da aka kama tare sun shirya yadda za su karɓi wani ɓangare na kuɗin da aka tara.

“An gaya mana cewa mahaifiyata tana da hannu a lamarin, kuma tana hulɗa da mutumin. An gano shi ne ta hanyar bin sawun waya, kuma sun shirya karɓar wani kaso daga cikin Naira miliyan 20 da aka tara,” in ji ta.

Ta bayyana cewa lamarin ya yi matuƙar girgiza ’yan uwansu, musamman ganin cewa mahaifinta na fama da rashin lafiya.

A nata ɓangaren, ƙungiyar Harmony Ladies Club, wadda Anita ke cikinta, ta bayyana takaicinta kan yadda lamarin ya kasance bayan ta bayar da tallafin kuɗi da sauran taimako domin neman ceton matar.

Mai magana da yawun Rundunar ’Yan Sandan Jihar Edo, CSP Moses Yamu, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce an kama mutum huɗu da ake zargi da hannu a lamarin.

“Zan iya tabbatar da faruwar lamarin, sannan an kama mutum huɗu da ake zargi da hannu a wannan al’amari,” in ji shi yayin da ya ce bincike zai ci gaba da gudana.