An kama ’yan bindigar da suka kashe jami’an FRSC 3 a Kebbi

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kebbi ta kama wasu mutum bakwai da ake zargi da kasancewa cikin ’yan bindigar da suka kashe jami’an Hukumar Kiyaye Haɗurra ta Ƙasa (FRSC) uku a kan hanyar Illo zuwa Tsamiya a makon da ya gabata.

A wata sanarwa da Kakakin rundunar ’yan sandan, SP Bashir Usman, ya fitar, ya ce uku daga cikin waɗanda ake zargin—Muhammadu Bande, Aliyu Abubakar da Muhammadu Aliyu—an kama su ne a yayin da suke kan hanyar kai kayan abinci ga wasu ’yan ta’adda da ke ɓuya a dajin Soda.

Sanarwar ta ce an cafke su ne ta hannun jami’an rundunar ’yan sandan kwantar da tarzoma a kan hanyar Illo zuwa Lolo, a wani aiki da aka tsara na rushe hanyoyin sadarwa da take tallafa wa ayyukan ’yan bindiga a jihar.

Ta ƙara da cewa “bisa sahihin bayanan sirri, jami’an ’yan sanda da ke sintiri a kan hanyar Illo–Lolo sun tare wasu daga cikin waɗanda ake zargin yayin da suke kan babur ɗin Haojue daga dajin Soda zuwa ƙauyukan da ke kan iyaka.”

Ya ce wasu mutum huɗu da ake zargi da kasancewa cikin ƙungiyar ’yan bindigar—Haruna Abubakar, Abubakar Lawali, Anme Shehu da Yahaya Shehu—an kama su a wani aiki daban da aka gudanar a yankin Bakin Ruwa zuwa Ka’oje.

Ya ce a dukkan waɗanda ake zargin na hannun ’yan sanda, kuma ana ci gaba da bincike.