An kashe jami’in tsaro, an yi sace mutum 10 a Sabon Birni

Wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa ya ce kimanin mutum 10 ne aka yi garkuwa da su a harin

An kashe jami’in tsaro, an yi sace mutum 10 a Sabon Birni

‘Yan bindiga

Wani jami’in Rundunar Tsaron Al’umma ta Jihar Sakkwato ya rasu, yayin da aka yi garkuwa da mutane da dama a wani harin ’yan bindiga a garin Sabon Birni da ke Ƙaramar Hukumar Sabon Birni ta Jihar Sakkwato a daren Litinin.

Majiyoyi da dama sun bayyana harin a matsayin sabon yinƙurin ’yan bindigar na kutsawa cikin garin, wanda a halin yanzu ke ɗauke da ɗimbin mutanen da suka rasa matsugunansu daga ƙauyukan da matsalar tsaro ta shafa.

Ɗan Majalisar Dokokin Jihar Sakkwato mai wakiltar Sabon Birni, Aminu Boza, ya tabbatar da harin, yana mai cewa an yi garkuwa da mutane da dama, amma ya ce har yanzu ba a tantance adadin mutanen da aka sace ba.

“Ba zan iya bayyana adadin mutanen da aka yi garkuwa da su ba, domin Sabon Birni ba ƙaramin gari ba ne. Wasu mazauna garin na iya tserewa zuwa cikin dazuka da ke kusa, yayin da wasu kuma wataƙila ba sa cikin garin a lokacin da harin ya faru. Sai bayan an gudanar da cikakken bincike ne za a iya tantance adadin waɗanda aka sace,” in ji Boza.

Wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa ya ce kimanin mutum 10 ne aka yi garkuwa da su a harin.

Ya ce, “Wannan shi ne karo na uku da ’yan bindiga ke ƙoƙarin kai hari Sabon Birni, kuma sun bi hanyar da suka saba amfani da ita a hare-haren da suka gabata.

“Sun kashe wani jami’in Rundunar Tsaron Al’umma tare da yin garkuwa da kusan mutum 10.”

Boza ya bayyana cewa harin ya faru ne a yankin Kantin Gabas, da ke bayan garin Sabon Birni kusa da filin Idi na al’ummar yankin.

“Ba za mu ce harin bai faru a Sabon Birni ba, domin wurin na bayan gari ne kuma shi ne filin Idi na al’ummarmu,” in ji shi.

A cewarsa, jami’in Rundunar Tsaron Al’ummar da aka kashe ya samu harbin bindiga a hannu a lokacin harin, kuma ya rasu ne yayin da ake kai shi asibiti a safiyar Talata.

Da aka tuntuɓi kakakin Rundunar ’Yan Sanda a Jihar Sakkwato, DSP Ahmad Rufa’i, ya ce har yanzu bai samu rahoton aukuwar lamarin ba, amma ya yi alƙawarin tuntuɓar jami’in da ke kula da ofishin ’yan sanda na yankin domin samun ƙarin bayani.