APC za ta ƙwace dukkan jihohin Kudu maso Yamma – Ganduje

Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa, jam’iyya mai mulki za ta ƙwace yankin Kudu maso Yamma ta hanyar lashe zaɓen Gwamnan Jihar Ondo da za a yi ranar 16 ga watan Nuwamba. Ganduje ya bayyana hakan ne a lokacin da ya jagoranci mambobin Kwamitin Zartarwa na Ƙasa (NWC) na Jam’iyyar […]

APC za ta ƙwace dukkan jihohin Kudu maso Yamma – Ganduje

Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa, jam’iyya mai mulki za ta ƙwace yankin Kudu maso Yamma ta hanyar lashe zaɓen Gwamnan Jihar Ondo da za a yi ranar 16 ga watan Nuwamba.

Ganduje ya bayyana hakan ne a lokacin da ya jagoranci mambobin Kwamitin Zartarwa na Ƙasa (NWC) na Jam’iyyar APC zuwa taron masu ruwa da tsaki a Akure, babban birnin jihar a ranar Lahadin da ta gabata.

Shiyyar Kudu maso Yamma ta ƙunshi jihohi shida da suka haɗa da Jihar Legas da Oyo, da Ondo da Ekiti da Osun da kuma Ogun. Duk jihohin in ban da Osun da Oyo Jam’iyyar APC ke mulkinsu, sai dai Jam’iyyar APC na samun turjiya daga Jam’iyyar PDP a zaɓen Gwamnan da za a gudanar a jihar.

Amma dai Jam’iyyar APC tana fatan ganin ta samu gagarumar nasara a Jihar ta Ondo tare da fatan ganin sauran jihohi biyu da ke hannun PDP a yankin sun koma nata.

Da yake jawabi a wajen taron, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya ce, jam’iyya mai mulki na aiki tuƙuru don ganin ta samu nasara a duk faɗin yankin kafin nan da zaɓen 2027 mai zuwa.

Ya kuma jaddada cewa, Jam’iyyar APC tana da dabarunta na ganin ta karɓe jihohin Oyo da Osun duk su kasance ƙarƙashinta, amma ba zai bayyana waɗannan dabaru ba, sai dai ya tabbatar da cewa, jam’iyyar za ta ci gaba da samun magoya bayan Shugaba Bola Tinubu, musamman a yankin Kudancin ƙasar nan.

A yayin da yake bayyana cewa jam’iyyar ba za ta bayyana dabarun da za ta bi wajen samun nasara a jihohin yankin ba, Ganduje ya bukaci shugabannin Jam’iyyar APC da su haɗa kai wajen tabbatar da haɗin kan ’ya’yan jam’iyyar.

Ya ce, zaɓen gwamna da za a yi a Jihar Ondo tamkar ci-gaba ne ga Jam’iyyar APC, inda ya ƙara da cewa, ɗaukacin shugabanni a matakin ƙasa sun nuna goyon bayansu ga gwamna mai ci Lucky Aiyedatiwa.

“A wannan yanki na siyasa, dole ne mu bayar da kashi 100 don goyon bayan APC.

“Don haka, dole ne Jihar Ondo ta kasance abin misali ga sauran jihohin biyu, Oyo da Osun za mu kama su, amma ba zan tona asirinmu ba.

“Muna shirya dabaru. Dole ne Shugaba Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya samu goyon baya ɗari bisa ɗari.

“A wannan zaɓe mai zuwa, muna goyon bayan Gwamna Aiyedatiwa. Mun yi shiri a matakin ƙasa don ganin an yi zaɓe cikin nasara.

“An kuma sanar da Gwamna Babajide Sanwo-Olu na Jihar Legas cewa zai shugabanci tawagar yaƙin neman zaɓen gwamnan.

“Wannan zaɓe aiki ne da ya kamata a yi. Wannan babban taron masu ruwa da tsaki ya ƙarfafa mu.

“Hakan ya nuna akwai haɗin kai a cikinjam’iyyar.

“Muna sa ran samun kashi 90 na ƙuri’u a zaɓen gwamna mai zuwa”, in ji Ganduje.

Ganduje ya roƙi ’yan jam’iyyar da suka yi takarar neman tikitin kujerar gwamna tare da Aiyedatiwa da su mara wa gwamnan baya a zaɓen da ke tafe.

A nasa ɓangaren, Gwamna Sanwo-Olu ya ce, jam’iyyar za ta ƙara ƙarfi ne idan jama’a suka haɗa kai, inda ya ce bai kamata a bari Jam’iyyar APC ta rasa kujerarta ba ga jam’iyyar adawa.

Haka kuma ya buƙaci duk wanda aka yiwa ba daidai ba, da ya ajiye komai a gefe domin samun nasarar jam’iyyar.

Ya kuma yi kira da a samu haɗin kai, don tabbatar da nasarar APC, inda ya ƙara da cewa, ya zama dole a martaba irin hoɓɓasan da tsohon Gwamna marigayi Rotimi Akeredolu ya yi, ta hanyar tabbatar da samun nasarar Jam’iyyar APC ta ci gaba da riƙe kujerar gwamnan jihar.

A nasa jawabin, Shugaban Masu Rinjaye a Majalisar Dattawa, Opeyemi Bamidele ya taɓo muhimmancin wannan taro na masu ruwa da tsaki, wanda ya zo a daidai lokacin da Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ke buƙatar a mara masa baya daga yankin Kudu maso Yamma.

’Yan takara da dama da suka shiga zaɓen fid-da-gwani da aka gudanar a ranar 25 ga watan Afrilu da sun haɗa da Cif Olusola Oke da Wale Akinterinwa da Oladunni Odu duk sun bayyana goyon bayansu ga samun nasarar jam’iyyar, inda suka kuma yi alƙawarin yin aiki tare da kuma yin kira ga magoya bayansu daga ƙananan hukumomi da su tabbatar sun ba da kashi 90 na dukkan ƙuri’unsu ga Jam’iyyar APC domin samun nasara.

NAJERIYA A YAU: Me Nasarar Shugaban Amurka Donald Trump Ke Nufi Ga Najeriya?

Biden ya taya Trump murnar lashe zaɓe

Kamala ta amince da shan kaye a hannun Trump

Shugabannin duniya na ci gaba da aika wa Trump saƙon taya murna