Atiku, Obi da Kwankwaso za su haɗe don kawar da Tinubu a 2027 — PDP

Shekarar 2027 ta yi nisa a yanzu, amma ku sani Jam’iyyar APC ba barci take yi ba.

Atiku, Obi da Kwankwaso za su haɗe don kawar da Tinubu a 2027 — PDP

Atiku da Tinubu da Kwankwaso da Obi.

Hoto: The Sun

Jam’iyyar PDP ta ce, manyan ’yan adawar kasar nan suna kokarin hadewa domin kalubalantar Jam’iyyar APC mai mulki a zaben 2027.

Mataimakin Sakataren Yada Labarai na Jam’iyyar PDP, Alhaji Ibrahim Abdullahi ne ya bayyana hakan a ranar Litinin a shirin Sunrise Daily na Channels Television.

Alhaji Abdullahi ya ce, Atiku Abubakar na Jam’iyyar PDP da Peter Obi na Jam’iyyar Labour da Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso na Jam’iyyar NNPP suna tattaunawa kan yiwuwar samar da kawance.

A game da ko jam’iyyar za ta yi kokarin dawo da Obi da Kwankwaso da sauran shugabannin da suka bar PDP, Alhaji Abdullahi ya ce, ana ci gaba da tattaunawa.

“Domin kun ga yadda Peter Obi ya tattauna da Atiku, sannan ya gana da El-Rufa’i,” in ji shi.

Ya ce, idan jam’iyyar ta samu dawo da jiga-jiganta, to, daya daga cikinsu zai amince da sauran, sannan za mu samu alkibla daya.

“Damuwarmu a matsayin jam’iyya da wadannan mutane da na ambata shi ne ceto ’yan Nijeriya daga wannan kunci da ta da hankali, ga yunwa da fatara da rashin tsaro da ke damun kasar nan.

“Kuna ganin rashin fahimta da rashin sanin ya kamata daga bangaren masu jagorancin kasar nan,” in ji shi.

Ya ce, “Haka wadannan mutane wato Atiku da Obi da Kwankwaso, manufarsu ita ce ceto Nijeriya, domin hakan ya fi komai muhimmanci a wajensu kuma shi ne burinsu.

“Idan Atiku ya ce zai tsaya takara muddin yana cikin koshin lafiya, abu ne mai yiyuwa.

“Idan ya ce haka, za mu ga yadda za mu tafiyar da lamarin kamar yadda muka saba gudanar da shi, kuma darussan da muka koya za su taimaka mana mu aiwatar da komai yadda ya kamata a wannan karo.

“ Amma wani abu da zan gaya muku shi ne, kamar yadda Atiku yake cewa idan har shi ya fi dacewa ya fitar da al’ummar kasar nan daga cikin wannan hali to yana fatan zai yi hakan.”

Sakataren ya kara da cewa, Atiku ya kuma ce, idan har ba shi ne ya kamata ya kawo wannan sauyi ba, to, zai hakura da yin takara.

Wannan hakki ne a gare shi a matsayinsa na mai bin dimokuradiyya, sannan a sani cewa Kundin Tsarin Mulki ya tanadi cewa, zai iya tsayawa takara a kowane lokaci.

Don haka, abin da yake ƙoƙarin gaya muku shi ne, babu abin da zai hana shi yin takara, domin wannan shi ne ainihin dimokuradiyya.

Sai dai ba wai yana nufin cewa zai tilasta wa jam’iyya ta tsayar da shi takara ba ne.

Alhaji Abdullahi ya ce, “Ina gaya muku a fili yake kuma a bayyane cewa Peter Obi ya cancanta, zai iya kaiwa gaci, kuma za mu tallafa masa idan ya samu tikiti.

“Haka Atiku ya cancanta, kuma idan ya samu tikitin, shi ma za mu mara masa baya da ba shi goyon bayan da ake bukata domin ceto ’yan Nijeriya.”

Da yake magana kan zaben da ya gabata, Abdullahi ya koka kan yadda jam’iyyar ta yi asarar kuri’u sama da miliyan daya, inda ya ce da Kwankwaso ko Obi sun ci gaba da zama a jam’iyyar da tuni sun wuce wajen da kuma matsalolin siyasa da tattalin arziki da ake ciki a yanzu da ba su faru ba.

Za mu kayar da su — APC

Sai dai da take mayar da martani, Jam’iyyar APC ta ce ba ta damu da ci gaban da aka samu ba, inda ta nanata cewa manyan ’yan siyasar na adawa na layi daya ne kuma ba za su taba haduwa a inuwa guda ba.

Daraktan Yada Labarai na Jam’iyyar APC, Alhaji Bala Ibrahim ya bayyana haka a hira da Aminiya ta waya, inda ya ce, “Ba su taba zama barazana ga APC ba ko kadan.

“Hasali ma Jam’iyyar APC za ta ji dadi idan har aka ce wadannan mutane sun sake fitowa takara don kuwa Jam’iyyar APC za ta yi musu kaca-kaca.

“Idan aka duba wadannan ’yan ukun wato Atiku da Kwankwaso da Obi su ne ’yan takara na dindindin, domin da Atiku ya sha kaye a zabe, shi ke nan dukkansu sun fadi,” in ji shi.

Ya ce, “Saboda haka, muna sane da wadannan mutane, kuma muna sane da duk wani shiri nasu, don haka za mu jira su.

“Shekarar 2027 ta yi nisa a yanzu, amma ku sani Jam’iyyar APC ba barci take yi ba.

“Ita siyasa hanya ce ta bayarwa da karba da kuma sulhu. Amma idan ka samu mutanen da suka zo siyasa da tunanin hanya daya, burinsu kawai su zama ’yan takara, to, irin wadannan mutane ba ’yan siyasa ba ne.”

“Matukar ba za ka yarda da wata jam’iyya ko mutum ba, kana ganin kanka a matsayin mutum daya da kai kadai ne ka iya, kuma idan ba ka samu wannan matsayi ba, babu wanda ya isa, to, babu yadda za a yi ka taka rawar gani a dimokuradiyya, domin shi tsarin dimokuradiyya gaba daya ya shafi ra’ayoyin masu rinjaye ne,’’in ji Bala.

Wike zai fuskanci kwamitin ladabtarwa a kan zargin yi wa PDP zagon kasa

Da yake tsokaci kan al’amuran da suka shafi ladabtarwa a cikin jam’iyyar, musamman bisa martanin da Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike ya yi cewa gwamnoni su ne ke kunno duk wata wuta da kuma yin zagon kasa ga tsarin siyasa, musamman a jiharsa ta Ribas, Abdullahi ya ce, “Ba mu ji dadin yadda al’amura suke gudana ba, amma dai mun yi imanin Wike namu ne.”

Ya ce, maganar da Wike ya yi ba su yi tsammanin zai fadi haka ba. Ba sa tare da shi a kan haka’.

Abdullahi ya bayyana cewa, nan ba da dadewa ba Ministan zai fuskanci Kwamitin Ladabtarwar PDP da Mista Tom Ikimi ke jagoranta kan zarge-zargen zagon kasa ga jam’iyya.

“Wike na daya daga cikin wadanda ake sa ran su fuskanci wannan kwamiti.

“Kwamiti ne da zai binciki batutuwan da muka karbi korafe-korafe a kansu da suka shafi jam’iyya da yi wa jam’iyyar zagon kasa.

“An tattara koke-koke masu yawa a kan Wike a ƙasar nan. ’Yan jam’iyyar sun ga bai kamata a ce har yanzu ba a dauki wani mataki a kanWike ba, a matsayinsa na dan Jam’iyyar PDP,’’ in ji shi.

Ya ce, tuni kwamitin ya rubuta takardar gayyata ga Wike, inda ya ce kwamitin ya fara zama don duba koke-koke.

Abba ya yi tafiya yayin da rikici ya dabaibaye NNPP a Kano

Kotu ta hana EFCC kama tsohon minista kan taƙaddamar fili

Isra’ila ta ɗaiɗaita yara sama da 400,000 a Lebanon — UNICEF

Ba zan ce uffan kan rikicin NNPP a Kano ba — Kwankwaso