HOTUNA: Kwankwaso da Dickson sun gana kan rikicin NDC a Kano

Wata majiya mai tushe ta ce zaman ya samar da fahimtar juna tsakanin ɓangarorin da ke takun saƙa.

HOTUNA: Kwankwaso da Dickson sun gana kan rikicin NDC a Kano

Ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya gana da Jagoran Jam’iyyar na ƙasa, Sanata Seriake Dickson, a gidansa da ke Guzape a Abuja ranar Talata.

Taron ya samu halartar ɗan takarar gwamnan Kano na jam’iyyar, Kwamared Aminu Abdussalam, da Shehu Wada Sagagi, Nasiru Garo da sauran manyan jagororin NDC.

A cewar mai taimaka wa Kwankwaso kan harkokin yaɗa labarai, Saifullahi Hassan, an tattauna kan hanyoyin ƙarfafa tsarin jam’iyyar, bunƙasa manufofin ci gaban ƙasa da kuma gina haɗin kai domin samar da ci gaba a Najeriya.

Sai dai ganawar ta zo ne a daidai lokacin da rikici ke ci gaba da addabar reshen jam’iyyar na Jihar Kano, inda ake samun saɓani kan shugabanci, zaɓen ’yan takara da kuma zargin mamaye harkokin jam’iyyar da wasu ɓangarori ke yi.

A baya, jam’iyyar ta bayyana cewa ɗaya daga cikin manufofin taron na Abuja shi ne sulhunta ɓangarorin da ke rikici da kuma tabbatar wa magoya baya cewa NDC na ci gaba da kasancewa tsintsiya maɗaurinki ɗaya duk da matsalolin da suka kunno kai a Kano.

Wata majiya mai tushe ta ce zaman ya samar da fahimtar juna tsakanin ɓangarorin da ke takun saƙa, kuma ana sa ran shugabannin jam’iyyar za su bayyana matsayar da aka cimma nan ba da jimawa ba.

Ana kallon halartar Kwankwaso a taron a matsayin wata alama da ke nuna muhimmancin da shugabancin jam’iyyar na ƙasa ke bai wa rikicin Kano, la’akari da tasirin jihar a siyasar Najeriya.