Kamfanonin jiragen yawo za su maka NAHCON a kotu kan badakalar N17bn

Kamfanonin Jiragen Yawo sun yi barazanar maka Hukumar Aikin Hajji ta Ƙasa (NAHCON) a kotu idan ba ta dawo wa mambobinta kudadensu Naira biliyan 17 ba.

Kamfanonin jiragen yawo za su maka NAHCON a kotu kan badakalar N17bn

Ƙungiyar Kamfanonin Jiragen Yawo na Aikin Hajji da Umrah ta Najeriya (AHOUN) ta yi barazanar maka Hukumar Aikin Hajji ta Ƙasa (NAHCON) a kotu idan ba ta dawo wa mambobinta kudadensu Naira biliyan 17 ba.

Da yake jawabi yayin wani taron manema labarai a ranar Litinin, Shugaban NAHOUN, Abdullateef Ekundayo Yusuf, ya ce NAHCON ta daɗe tana rike kudaden mambobinsu.

Ya ce kuɗaɗen sun hada da ajiyar gargaɗi da kuɗaɗen bizar da ba a yi amfani da su ba, da kuɗaɗen da aka biya fiye da ƙima da kuma kuɗaɗen ajiyar Umrah, da dai sauransu, wadanda hukumar ke rikewa ba tare da nuna alamar za ta biya ba.

Ya ƙara da cewa a shekarar da ta gabata kaɗai NAHCON ta karbi sama da Naira biliyan 2.7 a matsayin ajiyar gargaɗi daga hannun ’ya’yan ƙungiyar bisa yarjejeniyar cewa da zarar an kammala aikin Hajji da makonni biyu za ta dawo musu da kudaden, amma har yanzu shiru.

“NAHCON ta ƙi dawo mana  da kudaden, maimakon haka, nema  suke mu biya fiye da abin da suka karba a shekarar da ta gabata a bana.

“Hukumar ta amsa cewa ta riƙe kuɗaɗen mambobinmu amma kuma ta ki nuwa alamar tana da niyyar ta biya mu.

“Hasalima ba su cika alƙawarin da muka yi yarjejeniya a kai cewa za su wallafa sunayen kamfanonin da za a dawo wa kudaden ba,” in ji Yusuf.

“Sannan mambobinmu na bin NAHCON bashin Naira biliyan 15.

“Tsarin Gwamnatin Saudiyya shi ne bayan kowane aikin Hajji za a dawo wa kamfanonin kuɗaɗensu a bisa dalilai uku.

“Na farko kuɗaɗen hidimar da alhazai suka biya amma ba a yi musu ba, kuɗaɗen ayyukan da ba a yi su yadda ya aka yi alkawarin ba, kuɗin tsaron lafiyar tantuna.

“Tun 2022 mambobinmu suke bin bashin waɗannan kuɗaɗen.”