Mafitar Taƙaddamar Gwamnan Kano Da Shugaban Hisbah

Kurakuran Gwamna Abba da kuma dacewar abin da Sheikh Daurawaya yi kan lamarin Hukumar Hisbah

Mafitar Taƙaddamar Gwamnan Kano Da Shugaban Hisbah

Gwamnan Kano Abba da Sheikh Daurawa

A ranar Alhamis ne (29/2/2024) aka ga wani social media clip wanda a cikinsa Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, yake yi wa wani taron malamai a Gidan Gwamnatin Kano jawabi, a inda yake nuna rashin jin daɗinsa da yadda ya ce jami’an hukumar Hisbah suna bin mutane suna raɗewa da sanda, suna rungumar samari da ’yan mata suna jefawa a cikin Hillux kamar wasu awaki.

Washegarin wannan ranar kuma sai ga wani clip na Sheik Aminu Ibrahim Daurawa wanda a cikinsa yake bayyana cewar ya sauka daga shugabancin hukumar ta Hisbah tare da yi wa Maigirma Gwamna fatan alheri da samun nasara a irin aikin Hisbar da yake so ya gani.

Kamar yadda kowa zai zata, wannan saƙo na Sheik Daurawa ya yamutsa hazo.

Al’ummah ta kowane saƙo a ciki da wajen Najeriya sun yi ta taɓa alli da wanda za su iya domin neman ƙarin bayyani da sharhi da hasashen makomar al’amura.

Da har na kame bakina daga yin sharhi a kan al’amarin da nufin sai Zauren Haɗin Kan Malaman Kano ya yi zama ya fitar da matsaya.

Don haka kafafen yaɗa labaran da suka buga min sammako ba su samu jin ta bakina ba.

Amman daga baya hakan nan na haƙura na yi wa wadanɗa suka tuntuɓe ni daga baya bayani gwargwadon abin da kowace kafa ta ɓukaci ta yi tsokaci a kan al’amarin.

Kuma tunda ranar Juma’a ce, an yi kaciɓis da shirina na Zube Ban Ƙwarya wanda nake gabatarwa a Arewa Radio, sai naga wajibcin na faɗi fahimtata ta ƙashin kaina, kafin Zaure ya fitar da tasa matsayar.

Saboda amfanin waɗanda ba su samu jin shirin ba, ga taƙaitaccen jawabin da na yi wanda ya shafi ɓangarori uku: Maigirma Gwamna, Malam Aminu Daurawa, da kuma Hukumar Hisbah.

Abin Da Ya Shafi Gwamnan Kano

A fahimtata, Gwamna ya gamu da samun tuntuɓe guda huɗu a kan abun da ya faru:

1) Tuntuɓe na farko wajen yin maganar da ya yi da kansa.

A irin wannan bigiren, ba a son shugaba na ƙoli ya yi magana da kansa, saboda a matsayinsa na ɗan Adam zai iya yin daidai zai iya yin kuskure.

Shi ya sa a tsari na shugabanci yake da mataimaka a mataki daban-daban.

A wannan maganar, alal-misali, akwai Shugaban Hukumar Zartarwa ta Hukumar Hisbah, akwai Kwamishina mai kula da harkokin addinai, akwai mai magana da yawun gwamna da ba shi shawara a kan harkokin yaɗa labarai, akwai Sakataren Gwamnati.

Kamata ta yi wani a cikinsu ya bayyana ɓacin ran gwamna a kan abinda bai yi masa daɗi ba.

Idan aka ji shiru, al’umma ta karɓi maganar ke nan, daga nan idan yana so sai ya fito ya yi magana ya faɗi abin da yake so; amman idan aka ji kaya-kaya, sai wani jami’in ko kuma shi gwamna ya fito ya gyara yadda maganar take.

2) Kuskure na biyu wanda gwamna ya gamu da shi shi ne na rashin la’akari da lokacin yin maganar.

Yau kimanin wata huɗu da ƙaddamar da “Operation Kauda Baɗala.”

Duk abun da za a zargi hukumar Hisbah da shi na kuskure wajen gudanar da aiki an yi ya wuce, kuma sun karɓi gyaransu.

Sannan ba da daɗewa ba ne aka yi zargin cewa gwamnati ta sa an fito da wata ’yar Tik-Tok daga gidan gyaran hali ba ta hanyar bin doka da oda ba.

Ƙurar ba ta gama lafawa ba sai ga shi gwamna ya fito a bainar jama’a yana aibata aikin Hisbah na yaƙi da masu laifi irin na wannan ’yar Tik-Tok ɗin.

Don babu makawa wasu su yi zargin akwai hannun Gwamna wajen karya dokar fitar da waccan yarinyar.

3) Tuntuɓe na uku na Mai girma Gwamna shi ne yadda bayaninsa bai ƙunshi nuna fushi game da masu aikata laifuka ba a Kano, sai fushi game da ƙuntata musu da yake ganin ana yi.

Kuma Kano jiha ce mai tutiya da aiwatar da Shari’ar Musulunci wacce Maigirma Gwamna ke jagoranta.

4) Kuskure na ƙarshe wanda ya samu gwamna shi ne rashin alamun neman bayani daga Hukumar ta Hisbah game da abin da yake ganin kuskure ne a wajen aiwatar da aikinsu.

Dogaronsa guda ɗaya tal, shi ne ya ga clip wanda yake nuni da an taka haƙƙin ɗan Adam.

Amman babu bayani game da yadda aka samu wannan ɗan Adam ɗin, ko shi me ya yi har ya janyo aka yi masa haka ba.

Ban yi zaton akwai wani kwamishinan ’yan sanda da idan ’yan sanda sun yi wani abu, wanda ake ganin kuskure ne wajen gabatar da aikinsu da zai fito sarari ya soke su ba, kamar yadda mai girma gwamna ya yi wa ’yan Hisbah.

Matakin Da Malam Aminu Daurawa Ya Ɗauka

A fahimtata, Malam Daurawa ya yi daidai game da matakin da ya ɗauka ta fuskoki guda uku:

1) Na farko, Malam ya kare mutuncinsa. Saboda jawabin Mai Girma Gwamna kamar Vote Of No Confidence ne a kansa.

Kuma idan har za a yi shugabanci kamar yadda ya kamata, wajibi ne bayan gwamna ya bayyana wannan rashin jin daɗin nasa kuma ya bi baya da hukunci na ladabtar da wanɗanda yake ganin sun nuna rashin iya aiki.

Kamata ya yi ke nan ya sauke Daurawa da mataimakansa waɗanda suka jagoranci aikin da ya ɓata wa gwamna rai, don gobe kada a kuma yin abin da zai ɓata masa rai haka.

2) Na biyu, abin da Malam Daurawa ya yi shi zai kare wa Hisbah da ma’aikatanta ƙima kuma ya farfaɗo wa da ’yan Hisbah ruhin aikin, bayan da Gwamna ya yi musu guduma ya sanyaya musu jiki.

3) Fa’ida ta uku da Malam Daurawa ya ɗauka ita ce ta barin ƙofar sulhu a buɗe, saboda babu wata kalma ta fushi ko ɓatanci da ya ambata, kuma ya yi wa gwamna fatan alheri da kuma yin kyakkaywar addu’a, don haka ya nuna ba faɗa yake yi da kowa ba, amman yanayin da aka saka shi ne ba zai bayu ya iya ci gaba da aiki ba.

Kuma wannan haka ake yi a ƙasahen da aka cigaba.

Sai dai kawai ace ba a saba ji ko gani ba a ƙasarmu.

Abin da Ya Shafi Hisbah

Ko shakka babu da jawabin Gwamna da ajiye aikin Kwamanda sun girgiza ’yan Hisbah, sun kuma dankwafe karsashin aiki a zukatansu.

Sai dai kuma al’amarin ya sabunta soyayyar Hisbah da ma’aikatanta a zukatan mafiya yawan al’ummar Musulmi a ciki da wajen Najeriya.

Malamai da dama sun samu kiraye-kirayen waya daga ciki da wajen ƙasa ana neman lallai a hanzarta yin sulhu tsakanin Gwamna da Kwamanda, saboda jihohi da yawa suna da burin samun irin Hisbar Kano.

To Yanzu Ina Abin Yi?

Da farko yana da kyau da Maigirma Gwamna da Malam Aminu Daurawa su tuna cewar aikin Hisbah ba kamar sauran ayyukan gwamnati ba ne.

Aiki ne da Allah (SWT) ya wajabta wa al’ummar Musulmi da su tabbatar da shi a cikin al’umar Musulmi.

Kuma idan ba a yi shi ba, zai kama kafatanin al’umar da laifi.

Don haka babu maganar wani ya yi fushi da aikin ballantana ya soke shi.

Ba mu sani ba ma ko dalilin da ya sa Jihar Kano take cikin sauƙi na fitinar da aka jarrabi maƙwabtan jihohi da ita, ko a dalilin aikin Hisbah ne.

Kuma idan aka yi gangancin lalata aikin, watakila mu tsinci kanmu a halin da ba a fata, Allah Ya kiyaye.

Don haka, wajibi ne a samu masu shiga tsakani.

Gwamnati ta sauya matsaya a kan maganar, ba abin kunya ba ne. Hasali ma, kima ce zata ƙaru.

Haka kuma shi ma malamin idan ya koma ya ɗora daga inda ya tsaya ba faɗuwa ba ce, shi ma daraja ce ta samu.

Su kuma ’yan Hisbah wajibi a sabunta yi musu bita ta sanin makamar aiki, saboda sababbin da suka shiga aikin su samu sanin makamar aiki da yadda za su kauce wa duk wani abu da zai janyo ce-ce-ku-ce.

Su sani cewa idan suka cutar da aikin to fa Allah ba Zai ƙyale su ba, saboda cewar aikinSa suke yi.

Dole ne a inganta aikin ta yadda za a ga bambanci da aikin da yake na neman abinci ne kaɗai.

Muna fatan Allah Ya sa tuntuɓe ya zamo ɗungushen yin gaba, ba baya ba.

Wassalamu Alaikum wa rahmatullah.

Saidu Ahmad Dukawa

BUK

2/3/24