Mai juna biyu ta mutu a harin da Rasha ta kai Ukraine

Yaƙin da Rasha ta fara a Ukraine tun shekarar 2022 ya zama mafi muni a Turai tun bayan Yaƙin Duniya na Biyu.

Mai juna biyu ta mutu a harin da Rasha ta kai Ukraine

Aƙalla mutum uku ne, ciki har da wata mata mai juna biyu mai shekara 22, suka mutu sakamakon hare-haren da Rasha ta kai a Ukraine cikin daren Litinin zuwa Talata.

Ministan Harkokin Wajen Ukraine, Andriy Sybiga, ya ce an kashe mutanen ne a birnin Chuguiv da ke yankin Kharkiv a arewa maso gabashin ƙasar.

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Ukraine ta fitar da hotuna da ke nuna gobara na ci a wasu gine-gine da kuma wasu motoci da aka ajiye a wurin bayan harin.

Magajin garin Chuguiv, Galyna Minaeiva, ta ce an kai harin ne da makamai masu linzami da kuma jiragen yaƙi marasa matuƙi na Shahed da aka ƙera a Iran.

Ukraine ta zargi Rasha da ƙara kai hare-hare kan fararen hula bayan da, a cewarta, sojojin Moscow suka kasa cimma wasu daga cikin manufofinsu a fagen daga.

“Saboda gaza cimma manufofinta a fagen fama, Rasha na ƙara ta’addanci kan fararen hula,” in ji Sybiga, yana kirab ƙasashen duniya da su ƙara yi wa gwamnatin Rashar matsin lamba.

Lamarin ya faru ne sa’o’i kaɗan bayan shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky, ya gana da ƙawayen ƙasarsa a birnin Landan domin tattauna batun yaƙin.

A yayin taron, Firaministan Birtaniya, Keir Starmer, da shugaban Faransa, Emmanuel Macron, da kuma shugaban gwamnatin Jamus, Friedrich Merz, sun goyi bayan kiran Ukraine na a fara tattaunawar kai tsaye da Rasha domin kawo ƙarshen yaƙin.

Sai dai shugaban Rasha, Vladimir Putin, ya ƙi amincewa da tayin Zelensky na ganawar ido da ido domin neman mafita ga rikicin.

Yaƙin da Rasha ta fara a Ukraine tun shekarar 2022 ya zama mafi muni a Turai tun bayan Yaƙin Duniya na Biyu, inda dubban fararen hula da ɗaruruwan dubban sojoji suka rasa rayukansu.