Abin da ke janyo rigima da gwamnoni — Sanata Siyako
Taimakon al’umma shi ne dalilin yin siyasa, kuma kowannenmu ya shige ta don kawo wa al’umma sauki.
Sanata Anthony Siyako, Sanata ne da ke wakiltar mazabar Gombe ta Kudu a Majalisar Dattijai.
A zantawar da ya yi da ‘yan jaridu, sanatan ya yi bayani kan batun fara hakar man fetur a Arewacin Nijeriya da samar da hasken wutar lantarki da kuma yunkurin bude Cibiyar Nazarin Maganin Cizon Maciji.
Asibitin kula da cizon maciji na Kaltungo na fama da matsaloli, kama daga karancin ma’aikata likitoci, inda biyu ne kawai a asibitin ga rashin kayayyakin aiki da kuma rashin wutar lantarki da sauransu. Ko akwai abin da sanata ke yi kan wannan?
Ina cikin Kwamitin Kula da Lafiya na Majalisar Dattawa, tun da muka fara aiki na samar da allurai guda 150 kuma zan sake samar da wasu guda 300.
Na kuma gabatar da kuduri a yi Cibiyar Nazarin Maganin Cizon Maciji, don wannan cibiya duniya na sane da ita, a Majalisar Dinkin Duniya an santa, tana kan taswirar duniya.
Duk an san batun asibitin Kaltungo, ba zan fada muku kudin kowace allurar ba, suna da tsada sosai, kuma lokacin da mutanen asibitin suka zo karbar alluran, sun fada min cewa babu wuta.
Don haka muna kokarin duba yadda za mu yi, saboda ‘yan uwanmu da yawa suna mutuwa saboda cizon macijin, sannan kuma za mu yi gidauniya don a samu yadda za a rika ceto rayukan al’umma. Ka ga alluran nan za su ceci ran wanda maciji ya sara.
A wasu lokuta babambancin jam’iyya na hana ruwa gudu wajen gudanar da ayyuka a wasu jihohi kamar yanzu kai kana Jam’iyyar PDP, Gwamna Inuwa Yahaya yana APC. Ya ya tafiyarku take?
Mu dai muna zaune lafiya, gwamna yana yi wa mutane ayyukan alheri, ni ma ina yi sauran ‘yan uwana kowa na yin iyakacin kokarinsa.
Abin da yake jawo fada rashin ilimin siyasa ne, don in mutum ya san siyasa, sai ya duba me ya sa ake yin siyasa, sai ka ga makasudin yin siyasa shi ne don dan Adam ya samu saukin rayuwa.
Ya kamata mu taimaki al’umma shi ne dalilin yin siyasa, kuma kowannenmu ya shiga siyasa ce don ya kawo wa mutanenmu saukin rayuwa.
Ka ga manufarmu daya ce, wato kyautata wa al’umma da kawo musu ayyukan alheri da ci gaba. In haka ne me zai jawo fada sai dai jahilcin siyasa.
Akwai arzikin man fetur a tsakanin jihohin Bauchi da Gombe, sai dai tun bayan kaddamar da aikin a bara har yau shiru ka ke ji.
Ni dai ina kwamitin kula da mai, kuma a lokacin da ministoci ke kare kasafin kudi, abokin aikina a Majalisar Wakilai da ke wakiltar Yamaltu Deba ya ta da maganar kuma na goyi bayan sa, za mu bi wannan abu sau da kafa domin ganin an dawo aikin.
Duk da aikin ya fuskanci tafiyar hawainiya mai yiwuwa ne saboda sauyin gwamnati, kuma an zuba jari da yawa ba yadda za a yi a bar wannan aikin ya tsaya.
Ministocin sun bamu tabbacin cewa za a ci gaba da aikin, mu kuma ba za mu zauna ba, har sai mun ga ana hako mai komai ya tafi daidai da ikon Allah.
Yaya batun matsalar wutar lantarki a mazabarka. Wasu garuruwan sun fi shekaru goma ba su da haske lantarki.
Mun yi zabe a watan biyu aka kuma rantsar da mu a watan shida muka fara aiki a Majalisar Dattawa, amma tun kafin in hau kujerar sanata na sa kafa a kan wannan matsalar kuma Allah Ya sa Kamfanin samar da wutar lantarki na TCN sun samar mana da karamar tashar ba da wutar lantarki a Billiri.
Sai dai wannan karamar tashar ba za ta iya ba da hasken wuta ga yankin Tangale Waja yadda ake bukata, duk da yankin akwai wuta amma ba karfi ana samun wuta awa biyu ko awa uku a rana.
Don haka Kamfanin TCN ne ke da hakkin samar da karamar tashar ba da hasken wutar lantarkin, amma kuma hakki ne na Kamfanin rarraba wutar lantarki na JED su rarraba wuta gida-gida da sako-sako, kuma shi Kamfanin JED mai zaman kansa na ‘yan kasuwa ne, shi ne zai kafa turakkun rarraba wutar lantarki da wayoyin da ake bukata.
Da muka fahimci haka sai na je Abuja na samu mutanen kamfanin muka hada hannu da JED suka fara aiki. A yau an samu wuta an hada layin da ke da karfin wuta.
Wuraren da ke da turakun wutar lantarkin duk mun yi kokari an samar musu da wuta mai karfi, inda a kwanakin baya aka samu nasarar gyara duk layukan wutar lantarkin.
Sauran wadanda ba sa samun wuta mai karfi za mu dauko wuta daga karamar tashar da ke Billiri.
Wani kokari kake wa mata da matasa?
Tun bayan rantsar da mu bai kai mako guda ba na tara mata da matasa a filin wasa na Kaltungo fiye da su dubu 8, muka ba su tallafin kudi don su zama masu dogaro da kansu.
Kuma muka ce za mu karfafi matasa da mata su 800 da za su bunkasa sana’arsu ta hanyar rubanya musu jari kamar sau uku, wanda mafi karancin abin da mutum guda zai samu ya bunkasa jarinsa shi ne Naira 250,000.
Za a kuma a samu tallafi daga Gwamnatin Tarayya na Naira dubu 50 da kuma dubu 25, wanda mutane 1200 zuwa 1500 za su rika samu a kowene wata tsawon wata shida.
Mun raba shinkafa tirela takwas da kuma dabbobi fiye da 50.