An cafke kananan yara 5 kan ayyukan matsafa a Kwara
An kwace makamai da miyagun kwayoyi da kuma ganye da ake zargin tabar wiwi ce a hannun kananan yaran
’Yan sanda sun tsare wasu kananan yara maza uku da mata biyu kan zargin ayyukan kungiyar matsafa da kuma sace-sace a Jihar Kwara.
Kakakin ’yan sandan jihar, Ajayi Okasanmi, ya ce, “An kwace makamai da miyagun kwayoyi da kuma ganye da ake zargin tabar wiwi ce a hannun kananan yaran.”
- Kotu ta tsare Dokta Idris Dutsen Tanshi a gidan gyaran hali
- Matashi ya kashe kishiyar mahaifiyarsa da tabarya
Ya ce dubun kananan yaran ta cika ne a ranar 26 ga watan Afrilu a wata matattarar bata-gari da ke yankin Gambari/Oja Gboro.
Ya ce, “Bayan samun bayananan sirri jami’anmu suka kai samame a dabar da ke kusa da Kokewu-Kobere a unguwar Oja Gboro, inda su aka kama su biyar din.”
Ya ce an gano yaran mambobin wata kungiyar asiri ce da ke addabar jama’a suna kwace musu kayayyaki a yankin.