An cafke mutum 11 kan garkuwa da mutane a Abuja
Jami’an tsaro sun cafe wasu nutum 11 kan zargin garkuwa da mutane a sassan Babban Birnin Tarayya
Mutum 11 sun shiga hannu kan zargin garkuwa da mutane da kuma yi wa masu garkuwa da mutane leken asiri a sassan Babban Birnin Tarayya.
Mutanen da ake zargin sun fada komar jami’an tsaro ne a kananan hukumomin Kuje da Bwari a karshen mako zuwa ranar Litinin.
Wani mazaunin yankin Kawu da ke Karamar Hukumar Bwari, ya ce a ranar Litinin ne jami’an tsaro suka kai samame a unguwarsu da kuma kauyan Gaba inda “suka kama mutum hudu a Kawu da wasu biyu a kauyen Gaba.”
Wata majiyar tsaro ta shaida mana cewa wasu mutum biyar da ake zargi da yi wa masu garkuwa da mutane leken asiri sun shiga hannu a kauyen Sabo a Karamar Hukumar Kuje daga ranar Asabar zuwa Litinin.
- An rasa yara 2 da gidaje 1,100 a gobarar sansanin gudun hijira a Borno
- NAJERIYA A YAU: Yadda Yajin Aiki Ke Shafar Fannin Ilimi
Majiyar ta ce, “An kama su ne a samaen da muke yi domin ganin bayan ayyukan masu garkuwa da mutane a yankin Kuje da kewaye, kuma mun yi nasarar kama wasu makiyaya da wasu ’yan asalin yankin.’’
Wakilinmu ya nemi karin bayani daga kakakin ’yan sanda ta Abuja, SP Josephine Adeh, amma ta shaida masa cewa zuwa lokacin ba ta samu rahoto kan lamarin ba.
A kwanakin baya dai an yi garkuwa da wasu mazauna unguwar Sabo inda masu garkuwar suka nemi kudin fansa Naira miliyan 15.