An kama mutanen da suka sace hular sarauta da sandar mulkin basarake a Ogun
An kama mutanen ne da hular basaraken a tare da su
’Yan Sanda a Jihar Ogun sun ce sun sami nasarar kama mutum 3 da ake zargi da fasa kofar fadar marigayi Olu na Ogunmakin Oba James Sodiya, sannan suka yi fashi a ciki.
Aminiya ta rawaito yadda wasu barayi suka fasa fadar a farkon makon na sannna suka sace hular sarauta da kuma sandar mulki ta basarakn.
- Gwamnati ta rushe gidan galar da ake kokarin sake ginawa a Gombe
- Gwamnatin Kano ta rufe wasu asibitoci masu zaman kansu
Da take tabbatar da aukuwar lamarin ga ’yan jarida a hedkwatar ’yan sanda a Abeokuta, babban birnin Jihar a ranar Asabar, Kakakin Rundunar a Jihar, SP Omolola Odutola, ta tabbatar da kama mutanen.
Ta ce cikin daren Alhamis da ta gabata ne wadanda ake zargin suka fasa kofar fadar da ke garin Ogunmakin cikin Karamar Hukumar Obafemi-Owode inda suka sace hular sarauta da sandar mulki mallakar marigayi Oba James Sodiya da ya kwanta dama wata biyu da suka gabata.
Kakakin ’yan sandan ta ce an gano hular sarautar ce daga hannun wadannan mutane masu suna Oke Oladipupo da Amusa Kazeem da Johnson Oluwole.
Sai dai ta ce har yanzu suna ci gaba da binciken gano sauran kayan da aka sace musamman sandar mulkin.