An rufe Jami’ar Kogi saboda zanga-zangar ɗalibai

Daliban sun tare babbar ƙofar shiga jami’ar ne tun bayan haɗarin da ya yi sanadin mutuwar ɗaliban jami’ar biyar.

An rufe Jami’ar Kogi saboda zanga-zangar ɗalibai

Hukumomin Jami’ar Tarayya da ke Lokoja a Jihar Kogi, sun rufe jami’ar har zuwa wani lokaci domin daƙile ci gaba da asarar rayuka da dukiya.

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun magatakarda kuma sakatariyar majalisar Jami’ar, Dokta Rebecca Aimiohu Okojie, a ranar Alhamis kuma ta bayyanawa manema labarai a Lokoja.

Hukumar Jami’ar ta yi zargin cewa, ɗaliban sun tare babbar ƙofar shiga jami’ar ne tun bayan haɗarin da ya yi sanadin mutuwar ɗaliban jami’ar biyar a ranar Litinin, wanda ya sa shiga harabar jami’ar ke da wuya.

“Rufewar jami’ar ya biyo bayan asarar rayuka da ɗalibai biyar suka yi a wani mummunan haɗarin tirela a Felele, ranar Litinin 17 ga Fabrairu, 2025.

“Tun faruwar lamarin, ɗalibai sun tare ƙofar jami’ar duk da kakkausar murya daga gwamnatin jihar da kuma ƙoƙarin da hukumomin jami’ar suka yi na a kwantar da hankula.

“Saboda haka, bisa shawarar hukumomin tsaro na jihar da kuma daƙile ci gaba da asarar rayuka da dukiya, shugaban jami’ar bayan shawarwarin hukumar ta yanke, shawarar a madadin majalisar jami’ar cewa jami’ar, jami’ar da rassanta za a rufe su har sai baba-ta-gani. Ɗalibai za su bar wuraren karatu kafin ƙarfe 12 na rana ranar Alhamis, 20 ga Fabrairu.”