An samun gwarzon mai yaki da beraye a Pakistan

Shekarun da suka gabata mutanen birnin Peshawar ta kasar Pakistan sun yi fama da harin bama-bamai da satar mutane, amma yanzu abin da ya fi ci musu tuwo a kwaraya babu kamar beraye, don haka wani mutumin birnin, Naseer Ahmad ya jajirce wajen yaki da beraye. Wannan gwarzon al’umma, ya tanadi kurar baro da safar […]

An samun gwarzon mai yaki da beraye a Pakistan
An samun gwarzon mai yaki da beraye a Pakistan

Shekarun da suka gabata mutanen birnin Peshawar ta kasar Pakistan sun yi fama da harin bama-bamai da satar mutane, amma yanzu abin da ya fi ci musu tuwo a kwaraya babu kamar beraye, don haka wani mutumin birnin, Naseer Ahmad ya jajirce wajen yaki da beraye.

Wannan gwarzon al’umma, ya tanadi kurar baro da safar hannu, inda ’ya’yansa kananan uku ke raka shi duk inda ya nufa a fafutikarsa ta yaki da beraye. Naseer Ahmad ya smau nasar halaka beraye sama dubu 100 cikin watanni 18.
“Wannan manufa tawa (ta yaki da beraye) na fara aiwatar da ita ne, bayan da aka kwantar da matata a asibiti, a sanadiyyar cutar da ta kamu da ita, bayan bera ya cije ta,” a cewar Ahmad cikin hirar da ya yi da Kamfanin Dillancin Labarai na AFP, lokacin da yake bakin aikinsa na kisan beraye a unguwar Zaryab.
“Kudin maganinta ya kai Rupees dubu biyar (daidai da Dala 50), kimanin Naira dubu 10 ta Najeriya. An yi mata allurer rigakafin cizon bera. Tsawon bera yakan kai inci tara zuwa 12 in an hada da bindin. Kusan ko’ina ana samunsu, kan tituna ne, ko a shagunan kasuwa,” inji Ahmad.
Mai farautar berayen y ace sukan kai farmaki ne cikin dare, inda suke lalata kayan gida da na shaguna, su kuma gurbata abinci, bayan sun ciji mata da kananan yara.
A daidai lokacin da Ahmad ke kokarin kashe beraye shi da ’ya’yansa mata, wani mazaunin yankin gul Zada yna bi, yana like ramukan da beraye suka bula a gidaje.
Bayan ga lallata wuri da beraye ke yi, Zada ya ce sun ma halaka jariri dan uwansa.
“Sun ciji dan uwana, jariri dan shekara daya da rabi, amma da muka kai shi asibiti nan take ya mutu,” a cewar Zada, kamar yadda ya bayyana wa Kamfanin Dillancin Labarai na AFP
Duk da cewa mazauna wannan yanki na farin ciki da aikin da Ahmad ke yi, amma hukuma ba ta san yana yi ba, ballantan ta ba shi wani tallafin kudi.
“Ba ni da kayan aiki, kuma ba na smaun wata gudunmuwa daga gwamnati, duk da haka wannan ba karamin aiki ba ne da na sa a gaba,” inji Ahmad.