An sanya dokar takaita shiga Intanet a Koriya
A makon jiya ne wasu jami’o’i a kasar Koriya ta Kudu suka haramta wa dalibansu shiga shafukan Intanet da daddare, kamar yaddda kafar yada labarai ta Korea Times ta bayyana. Dokar dai za ta yi aiki ne a bangaren dakin kwanan daliban. Kodayake, daliban sun bayyana rashin jin dadinsu da matakin. A daya daga cikin […]
A makon jiya ne wasu jami’o’i a kasar Koriya ta Kudu suka haramta wa dalibansu shiga shafukan Intanet da daddare, kamar yaddda kafar yada labarai ta Korea Times ta bayyana.
Dokar dai za ta yi aiki ne a bangaren dakin kwanan daliban. Kodayake, daliban sun bayyana rashin jin dadinsu da matakin. A daya daga cikin jami’o’in da dokar za ta yi aiki, za ta fara ne daga karfe daya na dare zuwa shida na safe. Inda a tsawon wannan lokaci daliban ba za su iya shiga Intanet ba.
Mahukuntar jami’ar sun ce sun dauki matakin ne domin kare hakkin daliban da suke bukatar runtsawa. Wani dalibi ya ce abin da ya sa yake shiga Intanet a lokacin da sauran dalibai suke barci shi ne, ba shi da sukunin yin hakan da rana tsaka.
kasar Koriya ta Kudu dai tana cikin sahun kasashen da suka fi yawan masu hawa Intanet a duniya.