An yanke wa mai fasakwaurin da ta bai wa kwikwiyo maganin barci daurin wata hudu

Kotu ta zartar wa wata mata ’yar shekara 33,mai suna Sharon Tan Mei Hua daurin wata hudu a kasar Singafo, inda aka kama ta da laifin yin fasakwaurin ’yan kwikwiyo 13, wadanda nau’ukan ’ya’yan karnukan kasashen Japan da Malesiya ne. Matar ta boyekarnukan ne a cikin jakunkuna a karkashin mazaunin motarta kirar Nissan  Wata kotun […]

An yanke wa mai fasakwaurin da ta bai wa kwikwiyo maganin barci daurin wata hudu
An yanke wa mai fasakwaurin da ta bai wa kwikwiyo maganin barci daurin wata hudu

Kotu ta zartar wa wata mata ’yar shekara 33,mai suna Sharon Tan Mei Hua daurin wata hudu a kasar Singafo, inda aka kama ta da laifin yin fasakwaurin ’yan kwikwiyo 13, wadanda nau’ukan ’ya’yan karnukan kasashen Japan da Malesiya ne. Matar ta boyekarnukan ne a cikin jakunkuna a karkashin mazaunin motarta kirar Nissan 

Wata kotun gunduma ta tuhumeta da dura wa karnunkan maganin barci, sannan ta cusa su cikin jakunkuna, ta boye su a wurare daban-daban na cikin motarta kirar Nissan.
Tan wadda ta sama hada-hadar safarar karnuka a kasar Sin, ta amince da laifin da aka tuhumeta da shi, inda ta bayyana cewa, ta yi fasakwaurin karnukan ne don ta sayar ta samu kudi a kasar Singafo. Alkalin da ta yanke mata hukuncin daurin, Hamidah Ibrahim, ta bayyana cewa, fasakwaurin karnuka na tattare d ahadarin yada cututtukan da ka iya halaka al’umma. Sannan gas hi ta aikata laifin keta haddin dabbobi har 13.
Ita kuwa Tan da ke neman afuwa, ta bayyana cewa, tana da da dan shekara biyu d ake kasar Sin, kuma ta shafe watanni ba ta ziyarce shi ba. Ta ce, ta koyi darasi, don haka ba zata kara aikata laifin ba.