An yi garkuwa da matan shugaban karamar hukuma a Jigawa

’Yan bindiga sun kutsa gidan Shugaban Karamar Hukumar Kiyawa a Jihar Jigawa, Nasiru Ahmad, suka yi awon gaba da matansa.

An yi garkuwa da matan shugaban karamar hukuma a Jigawa

‘Yan bindiga

’Yan bindiga sun kutsa gidan Shugaban Karamar Hukumar Kiyawa a Jihar Jigawa, Nasiru Ahmad, suka yi awon gaba da matansa.

Maharasun sun shiga garin ne da dare suna harbi babu kakkauta, inda suka je gidan kai-tsaye suka tafi da matan su biyu.

  1. Ana zargin mai unguwa da fyade da sa wa yarinya cutar HIV a Jigawa
  2. An kama shi da buhu 300 na tabar wiwi

Jami’in Hulda da Jama’a na Rundunar ’yan sandan jihar, Lawan Adam, ya tabbaar da harin da aka kai ranar Juma’a da dare, wanda ya ce mutum bakwai dauke da bindigogi kirar AK-47 ne suka kai farin.

Ya bayyana cewa bayan samun kiran neman dauki, babban ofishinsu da ke Kiyawa da kuma hedikwatar ’yan sandan jihar da ke Dutse sun tura jami’ansu domin bin sawun ’yan bnindigar domin ceto matan shugaban karamar hukumar.

Rufe ‘boda’ ya kawo yunwa da rashin aiki a Arewa —CNG

Bin diddigi: Gaskiyar batun kai hari a Bankin CBN

NAJERIYA A YAU: Lakurawa muka kai wa hari a Sakkwato —Sojoji

Manyan alhinin Najeriya a 2024