An yi watsi da motar alfarma ta Lamborghini a sharjah

An yi watsi da motar alfarma ta Lamborghini, wadda kimar kudinta ya kai Dirhami dubu 750, wato daidai da Naira miliyan 18, inda aka ajiye ta a wani babban kantin sayar da kayayyaki na Palm Tower da ke kan titin Sharjah, da ke Hadaddiyar Daular Larabawa.Mutane sai zuwa suke yi suna daukar hoto a gaban […]

An yi watsi da motar alfarma ta Lamborghini a sharjah

Motar alfarma ta Lamborghini a SharjahAn yi watsi da motar alfarma ta Lamborghini, wadda kimar kudinta ya kai Dirhami dubu 750, wato daidai da Naira miliyan 18, inda aka ajiye ta a wani babban kantin sayar da kayayyaki na Palm Tower da ke kan titin Sharjah, da ke Hadaddiyar Daular Larabawa.
Mutane sai zuwa suke yi suna daukar hoto a gaban motar, wasu kuwa har rubuce-rubuce suka rika yi, inda aka samu rubuce-rubuce kamar haka: “Don Allah a wanke ni,” ko a “kirani idan ana son sayarwa.”
Wani mai kula da kanti a jikin ginin da aka ajiye motar, ya ce: “Na gaji da tambayoyin da mutane ke yi mini kan wannan mota, wato “Mene ne labatrin wannan mota? Ba ni da masaniya, ba wanda ya sani.
Shi kuwa jami’in tsaron da ke aiki a jikin ginin, ya bayyana cewa ’yan sanda na sane da motar, kuma ta yiwu ma har sun yanka mata haraji. “Na ga wani dan sanda yana rubutu a gaban motar – ta yiwu haraji ne.”
Wani da ya kawo ziyara wannan ginin ya tura hotunansa da motar a shafinsa na facebook. Wannan mota tad an wasan kwallon kafa ce, akwai alamar “kantin dan kwallo,” da tsarabe-tsaren ’yan kwallo a kusa da madubin motar. Sannan akwai kwalbar lemun ’yan wasa, da kwalin magani Panadol, da wasu takardu, wadanda suka hada da na otal din Burj Al Arab.
Bayanan da aka samu game da lambar motar, na nuni da cewa, an satota ne, kuma an taba kwaceta saboda mai tukata ba shi da lasisi. Motar dai na dauke da tarar dirhami dubu Naira (N250,000), bisa tuhumar laifin ajiyeta a inda bai dace ba.
dimbin mutane da dabbobi duk sun yi wa motar alama, ta hanyar sanya kafa ko tabata da hannye.

 

Abubuwan da ya kamata ku sani game da Zaɓen Edo

Ban zama Shugaban Kasa don na tara kuɗi ba — Tinubu

Babu buƙatar mu riƙa tsayar da motoci muna duba takardu — ’Yan sanda

‘Yan bindiga sun ƙone gidan mai da motoci 4 a Enugu