Attajirin Saudiyya ya sayi motar shekara 115 kan Naira miliyan 17

Wani attajirin Saudiyya ya sayi motar da aka kera shekara115, kan kudi Dala miliya dubu 100, ko sama da Riyal dubu 250, wato a kalla Naira miliyan 17. Motar dai an sayeta ne daga hannun wani tsohon Ba’amurke.“Na sayi wannan motar da aka kerata a shekarar 1899,” a cewar Hamad bin Nasser. “Na yi fafutika […]

Attajirin Saudiyya ya sayi motar shekara 115 kan Naira miliyan 17
Attajirin Saudiyya ya sayi motar shekara 115 kan Naira miliyan 17

Wani attajirin Saudiyya ya sayi motar da aka kera shekara115, kan kudi Dala miliya dubu 100, ko sama da Riyal dubu 250, wato a kalla Naira miliyan 17. Motar dai an sayeta ne daga hannun wani tsohon Ba’amurke.
“Na sayi wannan motar da aka kerata a shekarar 1899,” a cewar Hamad bin Nasser. “Na yi fafutika da ta shafe sama da shekara hudu ina nemanta. Sai Ahmad, wani daga cikin abokaina, ya taimaka mini na samu irin wannan mota, wadda da wuya a sameta, musamman ma saboda shi abokin nawa, mutum ne mai sha’awar motoci na musamman da kaya masu dadadden tarihi.
Da farko Ahmad ya nuna shakkun samun irin wannan mota da ake son sayarwa, amma sai ya yanke cewa zai taimaka wa abokinsa.
“Bayan da muka shafe shekara hudu muna ta nemanta,sai muka smau guda a wajen wani tso dan Amurka,” inji Hamad. “Sai dai ya ki sayarwa.mu dai ba mu gajiya ba. A karshe ya amince zai sayar, inda muka dade muna kulla ciniki. Mun dai karkare ciniki a kan Dala dubu 100. Motar dai yanzu tana can a ajiye a gidan kayan tarihin da na bude don tara motoci na musamman, al’amarin da ya kasance jigon manufa,” inji shi.
Wannan attajiri da ya sayi motar, ya bayyana cewa har yanzu za a iya hawanta, a tafiya a kan titi.
Ya ce, an sha yi masa tayi ya sayar,sabodaganin babu irin motar, amma na ki yarda.