Babu maganar haɗewa da wata jam’iyya — PDP

jam’iyyar PDP na iya samun nasara matukar za a gudanar da zaɓe na gaskiya da adalci a Najeriya.

Babu maganar haɗewa da wata jam’iyya — PDP

Jam’iyyar adawa ta PDP ta ce a halin yanzu ba ta tattaunawar haɗewa da wata jam’iyya ko ƙulla wata alaƙa mai kama da hakan.

Sakataren yaɗa labarai na jam’iyyar na ƙasa, Mista Debo Ologunagba, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar bayan taron Kwamitin Gudanarwar jam’iyyar karo na 587 na da aka gudanar ranar Talata a Abuja.

Olugunagba ya ce yayin da ƙofar  PDP a buɗe take ga dukkan ’yan Najeriya, ciki har da tsoffin mambobinta da suka sauya sheƙa zuwa wasu jam’iyyu, jam’iyyar ta ci gaba da zama mai ƙarfi da kuma farin jini.

A cewarsa, jam’iyyar na iya samun nasara matukar za a gudanar da zaɓe na gaskiya da adalci a Nijeriya.

“Jam’iyyarmu za ta aminta da duk wani dan Najeriya shigowa cikinta a ci gaba da fafutikar neman muƙamai a zaɓukan ƙasar nan.

“Wannan zai ƙara tabbatar da cewa jam’iyyar PDP za ta ci gaba da zama jam’iyyar da ta fi soyuwa a wurin mafi yawan ’yan Najeriya.

“Saboda haka ya kamata mambobinta da jiga-jigan PDP da kuma ƙasashen duniya su yi watsi da duk wani rahoto da ke nuna duk wani nau’i na haɗaka tsakanin PDP da kowace jam’iyyar siyasa, don haka ba ya cikin muradin jam’iyyarmu,” in ji shi.