Ba’indiye ya shekara 70 ba ci ba sha

Likitoci na kokarin tantance gaskiyar lamarin wnai Ba’indiye da ya yi ikrarin cewa, tsawon shekara 70 bai ci abinci ko ya sha ruwa ba. Babban abin mamakin ma shi ne kasancewarsa cikin koshin lafiya. Prahlad Jani, mazaunin birnin Ahmedabad ne, wanda kuma ya yi ikrarin cewa, tun yana dan shekara takwas rabon shi da cin […]

Ba’indiye ya shekara 70 ba ci ba sha
Ba’indiye ya shekara 70 ba ci ba sha

Likitoci na kokarin tantance gaskiyar lamarin wnai Ba’indiye da ya yi ikrarin cewa, tsawon shekara 70 bai ci abinci ko ya sha ruwa ba. Babban abin mamakin ma shi ne kasancewarsa cikin koshin lafiya.

Prahlad Jani, mazaunin birnin Ahmedabad ne, wanda kuma ya yi ikrarin cewa, tun yana dan shekara takwas rabon shi da cin abinci ko shan ruwa. Ya kuma yi ikrarin cewa ya samu albarkar aloli takwas. Don haka yake rayuwa ba tare day a ci wani abu ba, sai dai karfin da yake samu na bauta.
Tun daga ranar 22 ga Afrilun 2010 zuwa Mayun shekarar aka rika kula da shi a wani asibiti da ake kira Sterlin, mai zaman kansa. Kuma an yi gwaji a kan Prahlad Jani, wanda ya gudanar da gwajin shi ne Sudhir Shah, inda ya jagorancin gungun masu bincike na mutum 35, dasuka fito daga Cibiyar Nazari lafiyar gabobin jiki da fannonin kimiyya ta DIPAs da sauran kungiyoyi.
Gungun masu binciken,sun yi ta gwaje-gwajen da suka ahda da awon jinni da daukar hotunan sassan jiki a tsawon sa’o’I 24, tare da lura da shi ta na’urar daukar hotunan sirri ta CCTb.
A tsawon wannan lokacin dai da aka shammace shi ne, a ka ga ya baje a cikin rana, amma babu wata alama da ta nuna ya ci ko sha wani nau’I na abinci. Kuma shi daruwa sai dai in zai yi wanka.
Bayan kwanaki 15 ana gudanar da bincike, Cibiyar DIPAS sun tabbatar da cewa: “Jani na cike da koshin lafiya, wadda tafi tsararrakinsa. “Daraktan DIPAS, ya ce: Sakamakon binciken lafiyar Jani, “zai yi matukar taimaka wa al’umma,” Shi kuwa Farfesa Anil Gupta, na cibiyar bincike ta SRISTI, ya ce, akwai yiwuwar mutum ya rayu ba tare da abinci ba, inda zai rika dibako rayuwa a kan kitsen jikinsa. Don haka yace akwai sarkaka ko wani “siddabaru.”