Bayan wata 10, ’yan bindiga sun sako Dokta Ganiyat

’Yan bindiga sun sako likitar nan da suka sace a Jihar Kaduna, Dokta Ganiyat Poopola, bayan ta shafe wata 10 a hannunsu

Bayan wata 10, ’yan bindiga sun sako Dokta Ganiyat

’Yan fashin daji sun sako likitar nan da suka sace tare da da mijinta da ɗan ɗan uwansa a Jihar Kaduna, Dokta Ganiyat Poopola.

A ranar 27 ga watan Disamba 2013 ne aka yi garkuwa da su a gidansu da ke Kaduna, kafin daga bisani a sako mijin nata, Kamardeen Poopola wanda hafsan sojan ruwa ne a ranar 28 ga watan Maris, 2024.

Sai dai masu garkuwar sun ci gaba da riƙe yaron mai suna Abdulganiyyu tare da Dokta Ganiyat Poopola wadda likita ce a Asibitin Ido na Ƙasa da ke Kaduna.

Tsawon lokacin da ta shafi a tsare ya sa Kungiyar Likitoci Masu Neman Ƙwarewa ta Nijeriya (NARD) shiga yajin aiki domin matsa wa gwamnati lamba ta kuɓutar da ita.

A ranar Laraba ’yan bindigar suka sako ta, kamar yadda shugaban kungiyar NARD, Tope Zenith Osundara tabbatar.