Dalilan ƙara kuɗin Jami’ar Gombe — Gwamna Inuwa

Gwamnan ya ce ƙarin ya zama dole ne domin bai wa jami’ar damar samar da da ingantattun abubuwa.

Dalilan ƙara kuɗin Jami’ar Gombe — Gwamna Inuwa

Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya bayyana cewa ƙarin kuɗin makarantar Jami’ar Jihar Gombe (GSU) da kashi 120 cikin 100 ya zama dole domin tabbatar da ɗorewar ingancin ilimi a jami’ar.

Gwamnan ya bayyana haka ne yayin rantsar da kwamitocin gudanarwa na manyan makarantu da hukumomin gwamnati, inda ya jaddada cewa kuɗaɗen makaranta na GSU sun yi ƙasa sosai idan aka kwatanta da na sauran jami’o’in jihohin makwabta kamar Borno, Adamawa, da Bauchi.

“Muna mayar da hankali sosai kan ilimin firamare da sakandare, amma ilimin manyan makarantu yana da tsada sosai kuma yana buƙatar zuba jari mai tsoka.

“Ƙarin kuɗin da muka yi zai bai wa jami’ar damar ci gaba da bayar da ilimi mai nagarta,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa ƙarin kuɗin makarantar ya samu ne bisa buƙatun ƙungiyar malaman jami’o’i (ASUU) da sauran ƙungiyoyi, domin ƙara kuɗaɗen shiga don inganta jami’ar.

Gwamnan ya buƙaci ɗalibai da iyayensu su yi amfani da shirin lamunin ɗalibai na Gwamnatin Tarayya don samun sauƙin biyan kuɗaɗen makaranta.

“Haƙiƙa, ilimi ba asara ba ne. Ku nemi lamunin ɗalibai domin ku samu damar yin karatu, wanda zai taimaka wa jami’a ta bunƙasa,” in ji Yahaya.

Ya bayyana cewa Gwamnatin Jihar Gombe na bayar da goyon baya sama da sauran jihohi, amma har yanzu akwai buƙatar jami’ar ta nemo wasu hanyoyin samun kuɗaɗe domin tabbatar da ɗorewar ayyukanta da gogayya da sauran manyan makarantu.