Dan dabo ya ce zai batar da dogon ginin duniya na Burj Khalifa

Wani shararren dan dabo da ya samu lambar yabo ta rufa ido a Hadaddiyar Daular Larabarawa, Dokta Montaser Al Mansouri, ya na neman masu daukar nauyinsa, don gudar da dabon batan dogon ginin Dubai na Burj Khalifa, a cikin watan Disamban bana. Ya bayyana cewa zai batar da dogon ginin duniyar har na tsawon dakika […]

Dan dabo ya ce zai batar da dogon ginin duniya na Burj Khalifa

 Dokta Montaser Al Mansouri Wani shararren dan dabo da ya samu lambar yabo ta rufa ido a Hadaddiyar Daular Larabarawa, Dokta Montaser Al Mansouri, ya na neman masu daukar nauyinsa, don gudar da dabon batan dogon ginin Dubai na Burj Khalifa, a cikin watan Disamban bana. Ya bayyana cewa zai batar da dogon ginin duniyar har na tsawon dakika uku.
Dokta Montaser Al Mansouri, shi ne Balaraben farko da ya taba samun lambobin yabon kwarewa da shahara a harkar dabo na Merlin, sannan aka sanya shi cikin jerin wadanda za su samu babbar lambar yabon dabo ta duniya (Oscars of the Magic World), wadda kungiyar ‘yan dabon duniya (IMS) da ke Amurka ke karrama ’ya’yanta da ita a kowace shekara.
Shahararrun masu rufa ido da suka karbi irin wadannan lambobi sun hada da Penn & Teller da Criss Angel da Dabid Copperfield da Siegfried & Roy.
Al Mansouri ya yi ikrarin aiwatar da dabo da rufa ido har dubu 70, a tsawon shekara 76.
“Zan iya batar da Burj Khalifa har na dakika uku. Idan na samu wanda zai dauki nauyin shirin, zan gudanar da wannan shirin a cikin watan Disambar bana,” a cewar shahararren dan dabo, haifaffen Ras Al-Khaimah, kamar yadda ya bayyana wa jaridar dpress.

Abubuwan da ya kamata ku sani game da Zaɓen Edo

Ban zama Shugaban Kasa don na tara kuɗi ba — Tinubu

Babu buƙatar mu riƙa tsayar da motoci muna duba takardu — ’Yan sanda

‘Yan bindiga sun ƙone gidan mai da motoci 4 a Enugu