dan Saudiyya ya zargi aljannu da kunna gobara sau 21 a gidansa

Wani dan kasar Saudiyya ya zargi aljannu da kunna masa gobar a gida, har sau 21, cikin shekara uku; kuma ya ce yana yawan jin maganganun da ba ya iya fahimtar ma’anarsu a lokacin da gobarar ke ci.Mutumin mai suna Ibrahim Al Asiri, ya ce gobara 10 da jami’an kashe gobara suka kashe, amma sauran […]

dan Saudiyya ya zargi aljannu da kunna gobara sau 21 a gidansa

Wani dan kasar Saudiyya ya zargi aljannu da kunna masa gobar a gida, har sau 21, cikin shekara uku; kuma ya ce yana yawan jin maganganun da ba ya iya fahimtar ma’anarsu a lokacin da gobarar ke ci.
Mutumin mai suna Ibrahim Al Asiri, ya ce gobara 10 da jami’an kashe gobara suka kashe, amma sauran shi ya kashe su.
 “Matsalar it ace a duk lokacin da na zuba wa wutar ruwa sai ta kara ruruwa. A lokacin da nake kashe gobarar, na ji wasu kalamai cikin muryoyin da ba gane abin da suke fada ba, a bayan kofofin gidana,” inji shi, kamar yadda ya bayyana wa tashar talabijin ta MBC.
Ya ce ya kirga gobara sau 21 a gidansa, da ke Kudancin Saudiyya, a gubndumar Asir, inda ya yi ta fama da matsalar har tsawon shekara uku.
“Kusan kullum na kwanta barci, ina cike da damuwa, da tunanin wata gobarar na iya tashi a kowane sashe na gidana, kuma har yanzu babu bayani kamn musababbinta,” a cewarsa.
Jaridar Sada, ta ruwaito mai magana da yawun Hukumar Kashe gobara, yana cewa kwanan nan za su bayar da rahoto game da gobarar da ke tashi a gidan Asiri.
“Mun fitar da rahoton farko da ke nuni da cewa mai wannan gidan yana da yakinin cewa gobararsa aljanu ne ke haddasata, amma mu ba ma tsammanin hakan. Don haka za mu bayar da rahoton karshe da zai bayyana hakikanin abin da ke haifar da gobarar,” inji Kanal Mohammed Al Asimi.

Ban zama Shugaban Kasa don na tara kuɗi ba — Tinubu

Babu buƙatar mu riƙa tsayar da motoci muna duba takardu — ’Yan sanda

‘Yan bindiga sun ƙone gidan mai da motoci 4 a Enugu

Kwalara ta kashe fiye da mutum 300 a Sudan