Daya daga daliban jami’ar da aka sace a Katsina ta kubuta

Sai dai rundunar ba ta bayyana sunan dalibar da ta ceto ba.

Daya daga daliban jami’ar da aka sace a Katsina ta kubuta

’Yan sanda sun ceto daya daga cikin dalibai mata biyar da aka yi garkuwa da su a Jami’ar Tarayya ta Dutsinma da ke Jihar Katsina.

An yi nasarar ceto dalibar ce bayan wani samame da Rundunar ’yan sandan ta kai a ranar Litinin.

A cewar kakakin rundunar, ASP Abubakar Aliyu, an ceto dalibar wadda ba a bayyana sunan ta ba saboda dalilai na tsaro ne a kauyen Bilbis da ke Jihar Zamfara makwabciyar Jihar Katsina.

Ya jaddada kudirin rundunar na yin amfani da wadatattun kayan aiki don ceto sauran daliban hudu daga da aka yi garkuwa da su.

“Yayin da wadda aka ceto ke samun kulawar likita, Kwamishinan ’Yan sanda ya jinjina wa jami’an rundunar, ya kuma bukaci jama’a su rika taimakawa da bayanai masu muhimmanci don inganta tsaro,” in ji sanarwar.

A ranar 4 ga watan Nuwamba, 2023, mahara suka sace dalibai mata biyar a Jami’ar Tarayya ta Dutsinma, inda daga bisani ’yan sanda suka tabbatar da kama daya daga cikin wadanda ake zargi da sace daliban.

An sace daliban ne a gidansu da ke bayan makarantar Mariamoh Ajiri Memorial International daura da hanyar Tsaskiya.