Firayiministan Indiya ya sa ma’aikata na neman kamus

Fiye da makonni biyu da suka gabata manyan ma’aikatan kasar Indiya na ta fafutikar  neman kamus din Hindi, ta yadda za su samu kwarewa wajen yin rubutun byaanan ayyukan hukuma a cikin harshen kasar, kamar yadda Firayiminisat Modi ya yi alkawari a lokacin yakin neman zabensa.An dade da horar da manyan ma’aikatan Indiya a cikin […]

Firayiministan Indiya ya sa ma’aikata na neman kamus
Firayiministan Indiya ya sa ma’aikata na neman kamus

Fiye da makonni biyu da suka gabata manyan ma’aikatan kasar Indiya na ta fafutikar  neman kamus din Hindi, ta yadda za su samu kwarewa wajen yin rubutun byaanan ayyukan hukuma a cikin harshen kasar, kamar yadda Firayiminisat Modi ya yi alkawari a lokacin yakin neman zabensa.
An dade da horar da manyan ma’aikatan Indiya a cikin harshen Ingilishi, don haka mafi yawansu suna da digirgirori da shaidun difuloma daga manyan jami’o’in duniya, wadanda suka hada da Odford da Cambridge da Harbard.
A wannan karon dai suna sarayar da yammacinsu wajen binciken kalmomin harshen Hindi a cikin kamus, saboda sabon Firayiminista Nrendra Modi ya bayar da umarnin cewa duk wasu takardun bayanai na hukuma dole a rubuta su cikin harshen Hindi, tunda shi ne harshen da daruruwan miliyoyin Indiyawa ke magana da shi a Arewacin kasar Indiya. Duk da cewa mafi yawan manyan ma’aikatan kasar na magana da harshen Hindi, amma kadan ne daga cikinsu suka iya rubutu don ayyukan sadarwa.
“Ina cike da mamakin ganin yadda nike kwashe tsawon lokaci don nazarin kamus din Hindi,” a cewar wani babban jami’in gwamnati, wanda ya bukaci a sakaya sunansa, don kada sabuwar gwamnatin ta dauka yana sukarta ne. “’’Yar karamar wasika na daukata tsawon lokaci,” inji shi.
Wannan matsaya ta amfani da harshen Hindi a ayyukan gwamnati da Modi ya bullo da ita, ta jefa tsoro da shakku a tsakanin manyan ma’aikatan gwamnati, har ta kai ga suna barazanar yin watsi da dokar.
Duk da cewa shi kansa Modi bai cika yin turancin Ingilishi a baianar jama’a ba, amma yakan yi kokarin wajen samun natsuwa da tattara hankalinsa yayin da yake magana da harshen Hindi. Su kuwa manyan ma’aikata na can na guna-guni kan a dora musu wani sabnon nauyi.
Sabon Firayiminista dai ya fito daga cikin talakawan Indiya, domin mahaifinsa mai shayi ne. Kuma yana cikin masu kishin Hindi, a kungiyarsu ta Rashtriya Swayamsewak Sangh, wadda ke ganin Hindi yaren gwarazan Indiya. Bisa la’akari da wannan dalilin ake ganin Firayiministan ya yi amfani da siyasa wajen bullo da wannan doka.