Firayiministan Norway ya yi badda kama a matsayin direban tasi

An samu hoton bidiyon da aka tura a shafukan sadarwar Facebook da Twitter na Firayiministan Norway, Jens Stoltenberg, wanda ke nuni da yadda ya rika badda kama a matsayin dan tasi, don jin ra’ayin wadanda suka zabe shi game da salon mulkinsa.“Yana da matukar muhimmanci in san abin da al’umma ke tunani a kai. Kuma […]

Firayiministan Norway ya yi badda kama a matsayin direban tasi

Firayiministan Norway na tukin tasi da yammaAn samu hoton bidiyon da aka tura a shafukan sadarwar Facebook da Twitter na Firayiministan Norway, Jens Stoltenberg, wanda ke nuni da yadda ya rika badda kama a matsayin dan tasi, don jin ra’ayin wadanda suka zabe shi game da salon mulkinsa.
“Yana da matukar muhimmanci in san abin da al’umma ke tunani a kai. Kuma babu wani wuri da mutane ke furta ra’ayinsu kamar a cikin motar tasi,” inji shi.
Ya saki wannan hoton bidiyon ne a lokacin da yake yakin neman zabe, a babban zaben kasa mai karatowa ranar tara ga watan Satumbar bana.
Ya boye na’urar kyamarar daukar hoto a cikin motar, wadda ta rika tattara masa bayanai a kan ra’ayoyin al’ummar kasar.
Mista Stoltenberg, ya yi basaja da tufafin ’yan tasi din birnin Oslo, da bajensu, inda ya rika fita a kowane yammaci, cikin watan Yuni yana daukar fasinjoji. Ana cikin haka sai wata mata ta gano shi, ta gabatar masa da bukatar  ya yi wani abu kan albashin manyan masu rike da mukaman gwamnati, ta yadda za su daina tara miliyoyi, alhalin ba su cancanci hakan ba.”

Ban zama Shugaban Kasa don na tara kuɗi ba — Tinubu

Babu buƙatar mu riƙa tsayar da motoci muna duba takardu — ’Yan sanda

‘Yan bindiga sun ƙone gidan mai da motoci 4 a Enugu

Kwalara ta kashe fiye da mutum 300 a Sudan