Ganduje ya lashi takobin kare kujerar gwamnan Nasarawa da kotu ta kwace

Ganduje ya ce zai yi duk mai yiwuwa wajen ganin kotu ba ta karbe kujerar gwamnan Nasarawa ba

Ganduje ya lashi takobin kare kujerar gwamnan Nasarawa da kotu ta kwace

Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje

Shugaban APC na Kasa, Abdullahi Ganduje, Abdullahi Umar Ganduje, ya ce zai yi duk mai yiwuwa wajen kare kujerar Gwamnan Jihar Nasarawa, da kotu ta soke nasarar Gwamna Abdullahi Sule na jam’iyyar.

Ganduje ya yi alkawarin ne a taron liyafar da aka shirya wa shugaban APC na Jihar Nasarawa, Aliyu Bello, a garin Lafia.

Shugaban jam’iyyar na kasa wanda mataimakinsa Alhaji Muazu Rijau, ya wakilta, ya ce, “mu muka lashe zaben gwamnan Nasarawa kuma lallai za mu kare kujerarmu, domin Nasarawa Jihar APC ce, kuma da yardar Allah za ta ci gaba da zama a hannunmu.”

A nasa bangaren, Gwamna Abdullahi Sule da magabancinsa, Sanata Umaru Tanko Al-Makura; da kuma Sanata Ahmed Aliyu Wadada sun yaba wa shugaan jam’iyyar na jihar.

Gwamnan Sule ya ce tun daga shekarar 2011 a karkashin jam’iyyar CPC, kafin daga baya ta rikide zuwa APC, jihar Nasarawa ta fara samun cigaba da babu irinsa.

A nasa jawabin, Sanata Al-Makura ya ce ba babu shugaban jam’iyya da ya fi Bello dacewa a Jihar Nasarawa, don haka ya kara kira da a ba shi goyon baya yadda ya kamata.

Al-Makura ya kuma yi kira ga magoya baya da su yi watsi da duk wata ji-ta-ji-ta da ke iya kawo baraka a jam’iyyar ta APC.