Gobara ta ƙone gidaje, dabobbi da kayan abinci a Kano

Gobarar ta tashi ne sakamakon wutar dafa abinci da aka bari ba tare da an kashe ba.

Gobara ta ƙone gidaje, dabobbi da kayan abinci a Kano

Wata gobara da ta tashi (tsohuwar ajiya)

Wata gobara da ta tashi cikin dare a garin Satigal da ke Ƙaramar Hukumar Bunkure a Jihar Kano, ta ƙone gidaje da dama, dabbobi, da rumbunan ajiyar hatsi guda shida.

Sai dai kawo yanzu babu labarin rasa rai a gobarar.

A cewar wata sanarwa da Jami’in Yaɗa Labarai na shiyyar Rano, Rabi’u Kura, ya fitar, mazauna yankin sun haɗa kai wajen kashe gobarar da kuma ceton rayuka da dukiyoyi.

Bayan haka, an kai rahoton lamarin ga Sarkin Rano, Dokta Muhammad Isa Umaru, a fadarsa.

Hakimin Satigal, ya jagoranci wasu mazauna yankin zuwa wajen sarkin, inda suka bayyana cewa gobarar ta lalata gidaje guda shida, kaya, hatsi, dabbobi da kuma wasu kayayyakin amfanin yau da kullum da darajarsu ta kai ta miliyoyin Naira.

Rahotanni sun nuna cewa gobarar ta fara ne sakamakon wuta da aka yi amfani da ita wajen dafa abinci, amma aka bar ta ba tare da an kashe ba.

Sarkin ya jajanta wa waɗanda abin ya shafa kuma ya ba su tallafin Naira 200,000 domin rage musu raɗaɗin asarar da suka yi.

An tara Naira 16 a taron ƙaddamar da littafin IBB

Ba ni da hannu a kisan Dele Giwa — Janar Babangida

NAJERIYA A YAU: Dalilan Da Ba Za Mu Sauke Farashin Burodi Ba —’Yan kasuwa

Ɗaliba ta rasu yayin da gini ya rufta a GGTC Potiskum