Gwamnatin Yobe Ta Ɗauki Jami’an Kiwon Lafiya 42 Aiki

Gwamnatin Mai Mala Buni ya zuwa yanzu, ta gyara tare da gina sabbin cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko guda 142.

Gwamnatin Yobe Ta Ɗauki Jami’an Kiwon Lafiya 42 Aiki

Hukumar kula da lafiya a matakin farko ta Jihar Yobe ta dauki ma’aikatan jinya 42 aiki domin inganta ayyukan kiwon lafiya a jihar.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin hukumar Adamu Abba ya fitar a Damaturu.

Ya ce tuni babban sakataren hukumar Babagana Machina ya gabatar da wasikun nadin aiki ga ma’aikatan jinya da aka zabo wadanda suka kammala karatun horon su daga kwalejin jinya da ungozoma ta Shehu Sule da ke Damaturu.

Abba ya kara da cewa ma’aikatan jinya za su cike gibin ma’aikata a cibiyoyin kula da lafiya a matakin farko na kananan hukumomi 17 na jihar.

“Gwamnatin Mai Mala Buni ya zuwa yanzu, ta gyara tare da gina sabbin cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko guda 142 a fadin jihar tun daga shekarar 2019.

“Tun lokacin yakin neman zaben da karo na biyu gwamnan ya yi alkawarin samar da ingantaccen cibiyar kula da lafiya a matakin farko a mazabun 178 da ke Jihar Yobe.

“Saboda haka, wannan daukar ma’aikata da aka yi za su ƙara ƙarfin ma’aikata a cibiyoyin don inganta aikin na kiwon lafiya” in Jin Abba.

Sakataren hukumar, Babagana Machina ya taya ma’aikatan jinya murna yana mai umartar da su mayar da hankali wajen sadaukar da kansu ga ayyukansu.