Haɗarin mota ya laƙume rayuka 12 a Neja
Uku daga cikin mata huɗun da suka rasu a sakamakon haɗarin ’yan gida ɗaya ne.

Aƙalla mutum 12 — ciki har da mata huɗu da maza takwas — sun riga mu gidan gaskiya a sanadiyyar wani mummunan haɗarin mota da ya auku a kan hanyar Lapai zuwa Agaie da ke Jihar Neja.
Wani da lamarin na safiyar wannan Asabar ɗin ya faru a kan idonsa, ya shaida wa Aminiya cewa uku daga cikin matan da suka rasu ’yan gida ɗaya ne.
- Ambaliyar Ruwa: Gwamnatin Kano ta raba kayan tallafi
- Ɗan Abacha ya kare mahaifinsa bayan ƙaddamar da littafin IBB
Sai dai wasu fasinjoji uku da suka haɗa da mata biyu da direban motar sun tsallake rijiya da baya, inda a yanzu suke samun kulawa a Babban Asibitin Lapai.
Bayanai sun ce haɗarin ya auku ne bayan wata taho-mu-gama da aka yi tsakanin wata mota ƙirar bas ɗauke da fasinjoji 15 da kuma wata tirela a daidai ƙauyen Nami.
Da yake zantawa da Aminiya ta wayar tarho, direban motar, Mohammed Baba, ya ce lamarin ya auku ne a yayin da suke kan hanyar tafiya Ƙaramar Hukumar Katcha bayan sun taso daga tashar mota ta Kasuwar Gwari da ke birnin Minna.
Direban ya alaƙanta haɗarin da tsautsayi wanda ya ce ya auku ne yayin da direban tirelan ya yi yunƙurin ƙetare wata mota da ke gabansa, lamarin da ya janyo motocin suka yi karo da juna.
Sai dai ya ce tuni direban tirelan ya arce da bayan faruwar lamarin.
Kwamandan Hukumar Kiyaye Haɗura ta Ƙasa FRSC shiyyar Neja, Kumar Tsukwam, ya tabbatar da faruwar lamarin.