Hisbah ta rufe gidajen rawa a Katsina
Hukumar ta umarci ɗaukacin masu gidajen rawa da ke gudanar da harkokinsu a cikin dare a faɗin jihar da su rufe

Hukumar Hisbah ta rufe gidajen rawa da ke gudanar da harkokinsu a Jihar Katsina.
Hukumar ta umarci ɗaukacin masu gidajen rawa da ke gudanar da harkokinsu a cikin dare a faɗin jihar da su rufe.
Shugaban Hukumar, Dakta Aminu Usman ne ya bada umarnin tare da gargaɗin masu wuraren da matakin ya shafa.
Ya bayyana cewa ɗaukar matakin ya zama dole domin kare tarbiyya da dokokin addinin Islama da kuma barazanar tsaro a jihar.
- Jami’an tsaron al’umma 6 sun mutu a artabu da ’yan bindiga a Sakkwato
- NAJERIYA A YAU: Tanadin Dokar Kasa Kan Kirkirar Gwamnatin Bibiya A Kano
Sanarwar da ya fitar ranar Laraba ta bayyana cewa tabbatar da tarbiyya da kare dokokin Musulunci sun zama wajibi.
Ya ci gaba da cewa, “za a ɗauki tsattsauran mataki kan duk masu kunne ƙashi, kuma ann riga an umarci jami’an tsaro da su tabbatar da bin wannan sabuwar doka.”