Hukumar NFC ta kafa kwamitin shawarwari a kan Kannywood

Hukumar Kula da Shirya Fina-finai ta Najeriya (Nigerian Film Corporation; NFC) ta nada Malam Ahmed dahiru Beli Shugaban Hukumar Tace Fina-finai ta Jihar Kano a matsayin dan kwamitin ba da shawarwari ga sabon shugaban hukumar NFC na kasa a kan fina-finan Hausa. Malam  Ahmed Beli ya ce aikin wannan kwamiti shi ne bayar da shawarwari […]

Hukumar NFC ta kafa kwamitin shawarwari a kan Kannywood
Hukumar NFC ta kafa kwamitin shawarwari a kan Kannywood

Hukumar Kula da Shirya Fina-finai ta Najeriya (Nigerian Film Corporation; NFC) ta nada Malam Ahmed dahiru Beli Shugaban Hukumar Tace Fina-finai ta Jihar Kano a matsayin dan kwamitin ba da shawarwari ga sabon shugaban hukumar NFC na kasa a kan fina-finan Hausa.
Malam  Ahmed Beli ya ce aikin wannan kwamiti shi ne bayar da shawarwari da kuma nusar da shugaban hukumar NFC a kan harkar fina-finai musamman irin wadanda suka shafi fina-finan Hausa.
Ya ce: “Babbar dama ce ga masana’antar shirya fina-finan Hausa, domin za su samu taimako da kuma gurabe na karo ilimi da kuma horo daga wannan hukuma ta gwammnatin tarayya.  Ina kira ga ’yan fim su dage wajen kyautata wannan sana’a tasu.
Shugaban ofishin shiyyar hukumar NFC da ke Kano, Mista Godwin Gongs ya ce nan ba da dadewa ba hukumar za ta yi bikin kaddamar da mambobin wannan kwamiti a babbar hedikwatarta da ke garin Jos, Jihar Filato.