Hukuncin shekara dubu aka yankewa wanda ya boye ’yan mata uku tsawon shekara 10 a Amurka

Ariel Castro, wanda ya boye ’yan mata uku tsawon shekara 10,  yanke masa hukuncin zaman kurkuku na shekara dubu, bisda tuhuma kan aiakta laifukan da suka ahd ada yunkurin kisan kai da satar mutane da fyade da keta haddi. Wannan mutum dan shekara 53, wanda tsohon direban bas din makaranta ne, ya kalli daya daga […]

Hukuncin shekara dubu aka yankewa wanda ya boye ’yan mata uku tsawon shekara 10 a Amurka

 Ariel Castro wanda aka yanke wa hukuncin shekara dubuAriel Castro, wanda ya boye ’yan mata uku tsawon shekara 10,  yanke masa hukuncin zaman kurkuku na shekara dubu, bisda tuhuma kan aiakta laifukan da suka ahd ada yunkurin kisan kai da satar mutane da fyade da keta haddi. Wannan mutum dan shekara 53, wanda tsohon direban bas din makaranta ne, ya kalli daya daga cikin wadanda ya cutar a kotu.
Wannan shari’a da aka yanketa cikin sa’o’i hudu, bayan an saurari karar, masu bincike sun gabatar da hotuna abubuwan da ke cikin gidan Castro, wadanda suka hada da agogo mai kararrawa da sarkoki da ake ratayawa a tagogi.
Alkali Michael russo ya yanke masa hukuncin tafiyar gidan kurkuku na shekara dubu. Castro ya amsa laifukan duk da tuhume shi a kai. A lokacin da aka yanke mas awannan hukuncin, daya daga cikin matan da ya azabtar, ta bayyana irin halin da ta samu kanta. Michelle Knight, ta ce: “Shekaru sun tafi, a lokacin da take yi wa Casgro jawabi, cewa: “Na shafe shekaru 11 a cikin azaba. Yanzu kaima taka azabar za ta fara.”
Jami’an da suka gudanar da bincike a gidan Castro, sun samu sarkoki masu tsawon kafa 100 da kwado, tare da damin kudi da aka boye a cikin injin wanki.  Duk lokacinm da Mista Castro ya tara da wadannan ’yan mata, ya kan jefa musu kudi, sannan ya bayyana musu cewa ana biyanku kan wannan aikin da kuke yi, kamar yadda jami’an binciken Amurka na FBI, Andrew Burke ya bayyana
Wani likita masu tabin hankali, Dokta Frank Ochberg, ya bayyana cewa, irin wannan mummunan hali da mutum kan samu kansa a ciki da wuya ya manta. Don su ma tamkar daurin raira da rai aka yi musu.

Ban zama Shugaban Kasa don na tara kuɗi ba — Tinubu

Babu buƙatar mu riƙa tsayar da motoci muna duba takardu — ’Yan sanda

‘Yan bindiga sun ƙone gidan mai da motoci 4 a Enugu

Kwalara ta kashe fiye da mutum 300 a Sudan