‘Ina cigiyar mai hannu daya in aura’

Wani matashi mai lalurar hannu daya da ke zaune a unguwar Kwangiri da ke kasuwar Abbatuwa a Jihar Legas, mai sun Kabiru Inusa  ya ce ba zai yi aure ba muddin bai sami mai hannu daya irinsa ba.Ya yi alkawarin bayar da kyautar Naira dubu biyar ga duk wanda ya samo masa mace mai hannu […]

‘Ina cigiyar mai hannu daya in aura’

Kabiru Inusa wanda ya dage sai mace mai hannu daya zai aura.Wani matashi mai lalurar hannu daya da ke zaune a unguwar Kwangiri da ke kasuwar Abbatuwa a Jihar Legas, mai sun Kabiru Inusa  ya ce ba zai yi aure ba muddin bai sami mai hannu daya irinsa ba.
Ya yi alkawarin bayar da kyautar Naira dubu biyar ga duk wanda ya samo masa mace mai hannu daya ya aura.
Malam Kabiru Inusa  dan asalin unguwar Sabuwar Kasuwa da ke cikin Birnin Gwari ta Jihar Kaduna ne, wanda ke yin sana’ar kayan gwangwan, tare da tura baro da hannu daya, ya yi alkawarin ne yayin da yake tattaunawa da Aminiya a karshen makon da ya gabata.
Ya ce, ‘Babu shakka ina cigiyar mace mai hannu daya irina. Kuma duk wanda ya samo min ita zan ba shi Naira dubu biyar. Dalilin da ya sa nake son na auri mai hannu daya shi ne ba za ta raina ni ba, saboda ita ma hannu daya gareta, amma idan na auri mace mai lafiya wacce ba ta da wata nakasa za ta rika yi min gori saboda nakasar da nake da ita. Shi ya sa na dage sai ’yar uwata mai hannu daya zan aura.”
Malam Kabiru dan kimanin shekaru 25 a duniya ya  kara da cewa ba ya bukatar tsohuwa  da makauniya da kuturwa da kuma gurguwa.
‘Ba na bukatar kowace irin mace sai mai hannu daya iri na, domin ita za ta fi dacewa da ni. Shi ya sa ka ga ba na zuwa ko da hira wurin mata, domin gudun bacin rai. Ina shakkar zuwa saboda kada su yi min gorin hannu daya’. In ji shi.
Kabiru wanda ya yi ikirarin yin karatun Firamare a Birnin Gwari  ba ya karbar sadaka sai dai kyauta.
‘Ni ba na karbar sadaka saboda kaskanci take janyo wa mutum. Na sha fada da mutane a kan hanya idan suka ba ni sadaka. Amma idan ka ba ni kyauta zan karba saboda kyauta ce. Shi ya sa ka ga nake yin sana’ar gwangwan, kuma ni da kaina nake tura barona da hannu daya ba tare da wani ya tallafa mini ba’.
Ya bayyana cewa ya samu nakasa ne shekaru da dama da suka wuce saboda rauni da wani Bafulatani ya yi masa da makami yayin da suke fada a garin su.
Ya shawarci nakasassu su rika neman na kansu, domin a ganinsa nakasa ba hujja ba ce ta yin bara da zaman kashe wando.
‘Ya kamata mutanenmu su gane cewa barace-baracen da suke yi suna zubar wa da kansu mutunci tare da janyowa kansu kaskanci da kuma wulakanci. Za ka ga a nan  Legas mutanenmu Hausawa suna yin bara ana zagin su. Wani lokaci ma za ka ga wani da lafiyarsa da komai ya na bara a Legas. Ka ga wannan bai kamata ba,’inji shi
Ya bayyana cewa ya samu nasarori da dama sakamakon sana’ar da yake yi ta sayar da kayan gwangwan.

Ban zama Shugaban Kasa don na tara kuɗi ba — Tinubu

Babu buƙatar mu riƙa tsayar da motoci muna duba takardu — ’Yan sanda

‘Yan bindiga sun ƙone gidan mai da motoci 4 a Enugu

Kwalara ta kashe fiye da mutum 300 a Sudan

Tags