Indiya ta hana kona kashin shanu a kusa da ginin Taj Mahal

Gwamnatin Indiya ta hana konas kashin shanu a kusa gidan sarautar tarihi na Taj Mahal, saboda tsoron kada duwatsun alfarma da aka yi amfani das u wajen gina gidan ka da ya sauya launi, daga fari zuwa dorawa, kamar yadda jami’an hukuma suka bayyana. Hukumomi na ta fafutikar shawo kan illar gurbatar yanayi a kan […]

Indiya ta hana kona kashin shanu a kusa da ginin Taj Mahal
Indiya ta hana kona kashin shanu a kusa da ginin Taj Mahal

Gwamnatin Indiya ta hana konas kashin shanu a kusa gidan sarautar tarihi na Taj Mahal, saboda tsoron kada duwatsun alfarma da aka yi amfani das u wajen gina gidan ka da ya sauya launi, daga fari zuwa dorawa, kamar yadda jami’an hukuma suka bayyana.

Hukumomi na ta fafutikar shawo kan illar gurbatar yanayi a kan wnanan tambarin soyayya na karni na 17 da ke Arewacin birnin Agra, wanda a kowace shekara yak e daukar hankalin miliyoyin ’yan yawon shakatawa.
Manufar hana kona makashin shanun, it ace, don a rage yawan sinadarin carbon da ke sauka a kan bangon Taj Mahal, a cewar Pradeep Bhatnagar, Shugaban yankin da ake kira da sunan Taj (Taj Zone).
“Akwai damuwar cewa daga lokaci zuwa lokaci launin Taj Mahal na sauyawa,” inji Bharnagar, a hirarsa da Kamfanin Dillancin Labarai na AFP.
konannen busasshen kashin shanum shi ake amfani da shi a matsayin makamashin girki. Mata kan liliya kashin shanun tamkar kwallon kankana, sannan sun baje shi a jikin bango, al’amarin da aka saba gani a daukacin fadin Indiya.
Bincike ya nuna, cewa, dalilin sauya launin Taj Mahal shi ne kurar da ke damfare a sinadarin carbon. Wadanda suka gudanar da binciken sun hada da jami’o’i da masana dadaddun al’amuran duniya, wadanda suka fito daga kasar Amurka.
Bhartnagar ya ce mazauna yankin agra za a karfafa musu gwiwa kan su rika amfani da makashi mai tsafta, kamar kanazir ko fetur da dizel. Ana sa cimma wannan manufa nan da watan Yulin bana, kamar yadda kafofin yada labaran kasar suka ruwaito.