Zirin Gaza: Isra’ila ta kashe kwamandojin Falasdinawa 3
Jiragen Isra’ila sun kashe jagoran Hamas na yankin Khan Younis da wasu kwamandojin kungiyar da kuma Islamic Jihad
Jiragen Isra’ila sun kashe wasu kwamandojin mayakan Falasdinawa na kungiyoyin Hamas da Islamic Jihad.
A safiyar Lahadi Hedikwatar Tsaron Isra’ila ta sanar cewa ta jiragenta sun kashe Bilal Al Kedra, wanda shi ne kwamandan Hamas a yakin Kudancin Khan Younis.
- Shugabannin Hamas 5 da Isra’ila ta shirya kashewa
- Rikicin Gaza: Muhimman abubuwan da ya kamata ku sani
- Falasɗinawa miliyan ɗaya na rige-rigen ficewa daga Zirin Gaza
Isra’ila na zargin Bilal na daga cikin wadanda suka tsara harin ba-zata da mayakan Falasdinawa suka kai mata mako guda da ya gabata.
Harin na ranar Asabar shi ne hari mafi girma da muni da mayakan Falasdinawa suka kai mata a cikin shekara 75, inda suka kashe mutum sama da 1,200 suka jikkata wasu, tare da garkuwa da wasu 1,50, ciki har da sojoji.
Da farko Isra’ila ta sanar cewa sojojinta sun kashe wasu jagogori biyu na Hamas da Islamic Jihad, ta take zargi da mummunan harin na makon jiya.
Isra’ila wadda ta shafe mako guda tana luguden bama-bamai a yankin Zirin Gaza ta ce ta kai hare-hare 100 a kan cibiyoyin Hamas da Islamic Jihad a unguwannin Zeitoun, Khan Younis da kuma Yammacin Jabalia.
Falasdinawa sun kaddamar da harin ne a matsayin ramuwar gayya kan kisan gilla da Isra’ila ke wa ’yan uwansu, musamman a baya-bayan nan, tare da mamaye yankunansu a rikicin da ya ki ci, ya ki cinyewa.
Rikicin Falasdinawa da Isra’ila a takaice
Rikicin Isra’ila da Falasdinawa dai ya samo asali ne shekaru da dama da suka gabata, musamman bayan yakin duniya, inda Yahudawa suka yi kaura zuwa yankin Falasdinu, inda suke gani a matsayin kasarsu ta kaka da kakanni.
Sun yi kaura zuwa yanzkin ne bayan kisan kiyashi da suka fuskanta a hannun Shugaban Jamus, Adolf Hitler, wanda ya kashe Yahudawa sama da miliyan biyu.
Bayan dawowarsu yankin ne Larabawan Falasdinu suka ba su kimanin kashi 20 na kasar su zauna a matsayin baki, amma daga baya aka fara samu takaddama a tsakaninsu, Yahudawan suka fara ikirarin mallakar kasa, tare da neman kafa kasar Isra’ila.
A kan haka ne aka yi ta samun sabani, har masu ruwa da tsaki suka yi ta sanya baki, aka yi ta kulla yarjejeniya ba tare da haka ta cim-ma ruwa ba.
Daga bisani rikicin ya yi kamari, har ya kai ga yaki, inda bayan Isra’ila ta yi nasara, kasashen duniya suka amince da ita a matsayin kasa mai cin gashin kanta, amma suka ki amincea da Falasdinu a matsayin kasa.
Isra’ila ta ci gaba mamaye yankuna mafi yawa a kasar Falasdinu har da muhimman wurare kamar Masallacin Kudus, da wasni yanki da birnin Kudu, inda a halin yanzu abin da ta bar wa Larabawa (Falasdina) yankin Zirin Gaza mai fadin murabba’in kilomita 365, bai wuci kashi 20 na asalin fadin kasarsu ba.
Hakazalika, ita da kawayenta sun ki amincewa da bai wa Falasdinu ’yancin zama kasa mai zaman kanta, sannan tana ci gaba da mamaye sassan Zirin Gaza, inda take tashin Falasdinawa tana mallakawa Yahudawa.
A tsawon lokaci, bangarorin biyu na wa juna kallon hadarin kaji, inda Falasdinawa ke zargin Isra’ila da hare-haren cin zali, inda take kashe su da kuma tsare duk wanda ta ga dama, yadda ta ga dama.
A kan haka ne kungiyar mayakan sa-kai na Falasdinawa — Hamas da Islamic Jihad — ke fadan kare kai da daukar fansa a matakin soji, lamarin da ya sa Isra’ilar da kawayenta irin su Amurka da Tarayyar Turai suka ayyana Hamas a matsayin ’yar ta’adda.
Isra’ila tana zargin Hamas da Islamic Jihad da kai mata harin tsokana ko ta’addanci, abin da take cewa shi ne dalilinta na kai hare-hare domin kawar da kungiyoyin daga doron kasa.
A tsawon shekarun da Isra’ila ta kai hari, ta kashe Falasdinawa sama da 100,000, ta raba miliyoyi da gidajensu, baya ga dubban da take tsarewa, ko take jikkatawa.
Majalisar Dinkin Duniya ta kiyasta cewa mutum sama da 300,000 sun rasa gidajensu a harin mako guda da Isra’ila ta yi Gaza, inda Isra’ilar ta yanke wutar lantarki da ruwan sha da abinci da magani da man fetur da sauran abubuwan bukata, ta kuma hana shiga da fita.
Harin ramuwar gayyar da Falasdinawa suka kai wa Isra’ila a makon jiya da martanin da ta dauka dai sun raba kan kasashen duniya, inda mukarraban Isra’ila ke goyonta tare da zargin Hamas ta tayar da zaune tsaye.
Wasu kuma ke ganin zaluncin Isra’ilar daa tsawon shekaru ya ki ci ya ki cinyewa ne ya jawo, kuma muddin ana son kawo karshen rikicin, to ya zama wajibi a ba wa Falasdinawa ’yanci da kuma kasarsu ta asali bisa yarjejeniyar farko da aka yi.