Jami’an ’yan sanda za su rika lura da masu tukin ganganci a Abu Dhabi daga sama

Jami’an ’yan sandan saman Abu Dhabi da ke cikin Hadaddiyar Daular Larabawa za su rika farautar masu tukin ganganci daga sararin sama. Wadannan jami’an ’yan sanda na Abu Dhabi Police Air Wing, sun bayyana wa manema labarai shirinsu na kama masu saba wa dokokin hanya daga sama, ta hanyar amfani da na’urori da yin sintiri […]

Jami’an ’yan sanda za su rika lura da masu tukin ganganci a Abu Dhabi daga sama

Munanan hadurra a birnin Abu DhabiJami’an ’yan sandan saman Abu Dhabi da ke cikin Hadaddiyar Daular Larabawa za su rika farautar masu tukin ganganci daga sararin sama. Wadannan jami’an ’yan sanda na Abu Dhabi Police Air Wing, sun bayyana wa manema labarai shirinsu na kama masu saba wa dokokin hanya daga sama, ta hanyar amfani da na’urori da yin sintiri a cikin kananan jiragen sama.
Wadanan kananan jiragen sama an sanya musu na’urorin daukar hotunan bidiyo, wadanda za su iya daukar hotuna a kowane irin yanayi, har ma da daddare, ta yadda za su samu saukin damke masu saba doka a cikin dare.
An dauki wannan matakin ne, saboda a bayar da kariya ga matasa masu karancin shekaru da ke sha’awar tukin ganganci a kan tituna, sannan a shawo kan daukacin ayyukan da suka saba wa doka a kan titunan biranen masarautar. An kuma fito da wannan manufa ce don tabbatar da tsaro da kariya ga masu bin tituna, ta yadda za tafi lafiya, su dawo lafiya; kuma ta haka za a shawo kan yawan mace-mace da jin raunuka a hadurra ababen hawa da ke kan tituna.
Birgediya Hussain Ahmad AlHarithi, Daraktan ’Yan sandan Kula da Ababen Hawa da sintirin tituna, ya ce an tura kananan jiragen sama su rika yin sintiri a daukacin titunan masarautar. Wadannan kananan jirage za su rika daukar hotunan hadurra, sannan su aike da sakonni da taswirar wurin da ake samu hadarin mota. Kuma jiragen za su zakulo motoci da ke hawan tituna ba tare da lamba ba, ko kuma masu dauke da lambobin bogi, sannan a danka su ga jami’an’yan sandan Abu dhabi don a gurfanar da su a gaban shari’a.

Ban zama Shugaban Kasa don na tara kuɗi ba — Tinubu

Babu buƙatar mu riƙa tsayar da motoci muna duba takardu — ’Yan sanda

‘Yan bindiga sun ƙone gidan mai da motoci 4 a Enugu

Kwalara ta kashe fiye da mutum 300 a Sudan