Jami’in EFCC ya mutu a wurin fada da abokan aikinsa

Fada tsakanin jami’an EFCC kan ajiyar kaya ya yi ajalin dayansu mai mukamin Sufeto a Jihar Sakkwato.

Jami’in EFCC ya mutu a wurin fada da abokan aikinsa

Wani jami’in Hukumar Yaki da Masu Karya Tattalin Arziki (EFCC) ya rasa ransa a wani fada da ya barke tsakaninsa a abokan aikinsa a Jihar Sakkwato.

Kakakin EFCC, Wilson Uwujaren, ya bayyana cewa wasu jami’an hukumar gudu uku sun kaure da fada ne bayan takkada ta ta barke tsakaninsu a kan ajiyar wasu kaya.

Ya ce likitoci a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Usmanu Danfodio da ke Sakkwato ne suka tabbatar da rasuwar jami’in mai suna Sufeto Abel Isah Dickson a ranar 7 ga watan Mayu da muke ciki.

Da yake sanar da hakan a safiyar Talata, Uwujaren ya ce sauran mutum biyun na tsare a hannun ‘an sanda, bayan aukuwar lamarin a ranar 5 ga watan Mayun da muke ciki.

Amurka za ta sayar wa Saudiyya makaman dala biliyan 1.96

Majalisar Ukraine ta amince da sabuwar gwamnati

Salihu Lukman ya fice daga Jam’iyyar ADC

Kotu ta hana FRSC tare motoci a titunan Kano

Tags