Jaroslav Silhavy ya yi ritaya daga aikin kocin Jamhuriyar Czech

Matsi ya yi yawa a aikin kuma yana da girma.

Jaroslav Silhavy ya yi ritaya daga aikin kocin Jamhuriyar Czech

Jaroslav Silhavy, kociyan Czech da ya yi ritaya

Jaroslav Silhavy ya yi ritaya daga aikin kocin Jamhuriyar Czech, bayan kasar ta samu gurbin shiga Euro 2024.

Silhavy, mai shekara 62 ya kai kasar matakin daf da na kusa da na karshe a Euro 2020, wanda ya karbi aikin tun cikin Satumban 2018.

Jamhuriyar Czech ta samu gurbin shiga wasannin da Jamus za ta karbi bakunci a shekara mai zuwa, bayan da ta ci Moldova 3-0 ranar Litinin.

“Ko da yake muna cike da murna, tun a baya mun cimma matsaya tun kafin wasannin cewar kowa zai kama gabansa,” kamar yadda ya sanar.

“Na kuma sanar da shugaban hukumar kwallon Jamhuriyar Czech, Petr Fouska a kan lamarin. Matsi ya yi yawa a aikin kuma yana da girma – wani abu da na kasa ganewa. Hakan ne ya sa muka cimma matsaya.”

Silhavy ya ci wasa 26 daga karawa 56 da ya jagoranta, sai canjaras 10, da kuma shan kashi a karawa 20. Kasar dai ta yi ta biyu a rukuni na biyar a neman shiga Gasar Euro 2024.

Kocin dan kasar Jamhuriyar Czech ya horar da kungiyar Viktoria Plzen da kuma Slavia Prague.

Kafin Jamhuriyar Czech ta buga wasa da Moldova a ranar Litinin, kocin ya umarci ’yan wasa uku daga tawagar, su koma gida a cikinsu har da Vladimir Coufal na West Ham, wadanda suka je suka kwana a gidan rawa ranar Asabar.