Jeremiah Useni: Muhimman abubuwa kan ministan Abuja na zamanin Abacha

Ga wasu muhimmin abubuwa kan tsohon Ministan Abuja a zamanin Abacha, Laftanar-Janar Jeremiah Timbut Useni (murabus) wanda ya rasu bayan fama da jinya, yama ɗan shekara 81 a duniya.

Jeremiah Useni: Muhimman abubuwa kan ministan Abuja na zamanin Abacha

Ga wasu muhimmin abubuwa kan tsohon Ministan Abuja a zamanin Abacha, Laftanar-Janar Jeremiah Timbut Useni (murabus) wanda ya rasu bayan fama da jinya.

  • An haifi Jeremiah Timbut Useni ne a ranar 16 watan Fabrairu, 1943.
  • Ɗan asalin ƙabilar Tarok ne a Karamar Hukumar Langtang da ke Jihar Filato.
  • Ya shiga aikin soja tun yana ɗan shekara 14 a duniya, inda ya fara makarantar yaran soji (NMS) da ke Zariya.
  • Abokansa na kiran shi da laƙabin Jerry Boy, kasancewansa abokin tafiya nagari kuma mai haba-haba da jama’a.
  • Shi ne tsohon Gwamna tsohuwar Jihar Bendel na mulkin soja daga shekarar 1984 zuwa 1985.
  • Ya kasance tsohon Ministan Sufuri a zamanin mulkin soji.
  • Ya riƙe muƙamin Kwata Masta-Janar na Rundunar Sojin Najeriya.
  • Shi ne Ministan Babban Birnin Tarayya daga 1993 zuwa 1998, zamanin tsohon shugaban mulkin soja Marigayi Janar Sani Abacha.
  • A zamanin mulkin farar hula ya shiga siyasa kuma ya lashe zaɓen Sanata mai Wakiltar Mazaɓar Filato ta Kudu a Kudu a Majalisar Dattawa daga 2015 zuwa 2019.
  • Ya rasu ranar Alhamis 23 ga watan Janairu, 2025 yana da shekara 83.