Karen da ya bace a ambaliyar Filifins ya bayyana bayan shekara guda

Wata mata’yar kasar Filifins ta gano karenta wanda ya bace bayan da aka yi ambaliyar ruwa da guguwa a ranar 8 ga Nuwambar bara. Wannan kare ya bace tsawon shekara guda, kamar yadda mai Karen Ailyn Metran ta bayyana wa Kamfanin Dillancin Labarai na AFP.“Ban taba hakura ba. Ubangiji ya ceci Bunny bayan guguwa da […]

Karen da ya bace a ambaliyar Filifins ya bayyana bayan shekara guda
Karen da ya bace a ambaliyar Filifins ya bayyana bayan shekara guda

Wata mata’yar kasar Filifins ta gano karenta wanda ya bace bayan da aka yi ambaliyar ruwa da guguwa a ranar 8 ga Nuwambar bara. Wannan kare ya bace tsawon shekara guda, kamar yadda mai Karen Ailyn Metran ta bayyana wa Kamfanin Dillancin Labarai na AFP.
“Ban taba hakura ba. Ubangiji ya ceci Bunny bayan guguwa da ambaliyar ruwa, don haka ba zan kayle shi ya mutuba,” inji ta.
Metran da mijinta suin gano Karen ne duk ya rame a cikin tarin shara, a tsakiyar birnin Tacloth,cikin watan da ya wuce.
Wannan birni na Tacloth ya yi fama da guguwa da ambaliyar ruwa da ta addabi Kudu amso Gabashin nahiyar Asiya, al’amarin da ya zama sanadiyyar mutuwar mutum sama da dubu akwaiko kuma suka bace.
“Mun hango kare ya yi dukun-dukun, wanda ya yi kamada nawa. Sai na kira sunan karyar, nan da nan ta biyo ni, tana so in rungumeta,” a cewar Metran.
Metran ’yar shekara 34, wadda ma’aikaciya ce a Kamfanin Inshorar Lafiya, ta ce ita da iyalinta sun gudu daga garin Taclothan kafin guguwa ta baibaye garin, inda suka bar karnukansu uku.
Biyu daga cikin wadancan karnuka sun nutse a ruwa, amma Bunny ya tsira, inda ya dawo wurin iyayen gidansa, ya shigo har dakin kwnaciyarsu.
“Mafi yawan mutanen da suka yi asarar kusan komai nasu a wannan ambaliyar, karnukan da suka bari a garin alamu ne na rayuwarsu a wurin,” a cewar Anna Cabrera, Babbar Daraktar kungiyar Kula da Walwalar dabbobi a kasar Filifins.