kungiyar kwallon kafa ta dauki nauyin auren nakasassu 107 a Saudiyya

kungiyar kwallon kafa ta Al-Hilal da ke kasar Saudiyya, ta dauki dawaniyar aurar da nakasassu 107, tare da hadin gwiwar kungiyar taimakon kan al’umma ta Harakiyyah. An kiyasta dawaniyar kashe kudi a auren da ta kai Riyal miliyan biyu da dubu 260. Kuma bayan an kamala bikin auren, kowane daya daga cikin ma’auratan zai samu […]

kungiyar kwallon kafa ta dauki nauyin auren nakasassu 107 a Saudiyya
kungiyar kwallon kafa ta dauki nauyin auren nakasassu 107 a Saudiyya

kungiyar kwallon kafa ta Al-Hilal da ke kasar Saudiyya, ta dauki dawaniyar aurar da nakasassu 107, tare da hadin gwiwar kungiyar taimakon kan al’umma ta Harakiyyah. An kiyasta dawaniyar kashe kudi a auren da ta kai Riyal miliyan biyu da dubu 260. Kuma bayan an kamala bikin auren, kowane daya daga cikin ma’auratan zai samu tallafin kudi har Riyal dubu 396, cikin shekara guda, don syaen kayan aikin gida, wadanda suka hada da na’urorin lantarki da tukwanen girki da kayan alatun gida.
Shugaban kungiyar Al-Hilal, Yarima AbdulRahman bin Mosaed da Muhammad Al-Motawwa na Harkiyyah, sun halarci bikin, wanda shi ne karo na biyar da kungiyar ta shirya aurar da dimbin mutane a lokaci guda.
A kalla mata 83, wadnada ba su da wata nakasa suka auri nakasassun, inda takwas daga cikin matan suka zama mata ta biyu. Sannan amare 12 daga cikin matan ba ’yan asalin kasar Saudiyya b ane.
A cewar Al-Motawwa, an shirya aiwatar da wnanan bikin aure ne, tare da tallafin kungiyar Al-Hilala kimanin shekara biyar da suka wuce, inda al-Hilal ta dauki nauyin auren bana, a matsayin tlalafin da suke bai wa al’umma.
Yarima Abdul Rahman ya ware kudin tallafi da daukar dawainiyar aurar da nakasassu, har Riyal dubu 500.
Da yake karin haske game da jawabin Yarima, Al-Motawwa ya roki manyan kungiyoyi da kamfanoni da su kaddamar da asusun tallafa wa ayyukan jin kan al’umma har guda 10 da kungiyarsa ke aiwatarwa, wadanda ya ce kimarsu daidai take da ta aure.