Limamin cocin da ya farfado daga sumar watanni 17 ya Musulunta

  Wani limamin darikar Katolika dan kasar Spain mai shekara 83, da ya shafe shekara 43 yana wa’azi a tsibirin Jaba da ke kasar Indonesiya, kuma kwararre a harshen kabilun yankin, ya yi fama da ciwon zuciya, a lokacin da yake taimaka wa wasu talakawa su gyara rufin gidansu, a sakamakon fadowa daga bene mai […]

Limamin cocin da ya farfado daga sumar watanni 17 ya Musulunta
Limamin cocin da ya farfado daga sumar watanni 17 ya Musulunta

 

Wani limamin darikar Katolika dan kasar Spain mai shekara 83, da ya shafe shekara 43 yana wa’azi a tsibirin Jaba da ke kasar Indonesiya, kuma kwararre a harshen kabilun yankin, ya yi fama da ciwon zuciya, a lokacin da yake taimaka wa wasu talakawa su gyara rufin gidansu, a sakamakon fadowa daga bene mai hawa biyu.
Malamin addinin mai suna Fada Eduardo bincenzo Maria Gomez ya Musulunta bayan da ya farfado daga sumar da ya yin a tsawon shekara daya da wata biyar. Domin a cewarsa:
“Ban san komai game da Musulunci ba. Ban taba karanta Alkur’ani ba, amma Allah ya cusa maganarsa a gare ni, inda ya bukaci in zama mai biyayya a Gare Shi, ta hanyar hasken da na gani, wato kofar zinari ta shiga aljanna da ta bayyana a gare ni. Sannan Allah Ya sanar da ni sunanSa Allah,” kamar yadda ’yan jaridar Kalimatan Press suka ruwaito daga bakin dattijon.
Wannan mutumin da ya yi fama da rauni a lakarsa, amma duk da haka ya samu ya mike, har ma likitocin da suka kula da lafiyarsa a Cibiyar Kula da Lafiya ta Kudancin Jakarta, sun bayyana cewa shi ne tsoho dan shekara 80 mai karfin jiki da suka taba gani a rayuwarsu. Domin da wuya a ce kasusuwansa ba su yi rugu-rugu ba,” a cewar Jim Won May, wanda ya dade yana aikin likitanci a shekaru sama da 20.
Musuluntar wannan dattijo ta bai wa mabiyan majami’arsa matukar mamaki, amma dai abin da ya fi komai mamaki shi ne, kimanin rabin kiristocin da ke majami’arsa sun nuna matukar sha’awarsu ga Musulunci. “Idan har Allah shi ne Ubangiji na gaskiya, to ba na son kasancewa cikin batattu a ranar kiyama. Na gaskata Fada Eduardo. Muna da tabbaci a kansa,” a cewar daya daga cikin mabiyansa.
Wannan tsohon limamin majami’a da ke karkashin kulawar jami’an lafiya, ya bayar da umarni a gina sabon masallaci, kuma har mabiyansa sun fara aikin tara kudin gudanar da aikin. “Muna masu biyayya ga Fada Eduardo a kan duk abin da ya umarce mu,” a sharhin daya daga cikin masu ibada a tsohon cocin Katolikan da yanzu aka sanya shi a kasuwa.