Masu kare hakkin dabbobi sun kalubalanci ministan da ya yi hadayar awaki 29 a Indiya

Masu fafutikar hakkin dabbobi sun kalubalanci ministan da ya yi hadayar awaki 29 a IndiyaMasu fafutikar kare hakkin dabbobi a kasar Indiya, sun kalubalanci Ministan Harkokin bude ido da Yawon shakatawa na kasar, Mista Suresh Paswan, wanda bayan an nada shi kan mukamin ya yi hadaya da awaki 29, a dakin bautar addinin Hindu da […]

Masu kare hakkin dabbobi sun kalubalanci ministan da ya yi hadayar awaki 29 a Indiya
Masu kare hakkin dabbobi sun kalubalanci ministan da ya yi hadayar awaki 29 a Indiya

Masu fafutikar hakkin dabbobi sun kalubalanci ministan da ya yi hadayar awaki 29 a Indiya
Masu fafutikar kare hakkin dabbobi a kasar Indiya, sun kalubalanci Ministan Harkokin bude ido da Yawon shakatawa na kasar, Mista Suresh Paswan, wanda bayan an nada shi kan mukamin ya yi hadaya da awaki 29, a dakin bautar addinin Hindu da ke Bihar.
Kafafen yada labarai sun ruwaito yadda ministan, tare da magoya bayansa, suka ziyarci wurin ibada da ke karshen Gabashin Jihar Bihar, a gundumar Jamu, inda suka yanka awaki 29, a kan dandamalin tsayuwar limaminsu, wadda ya rika yi musu wakokin yabon abin bautarsu.
Daga cikin magoya bayan Ministan, akwai wani babban jami’in ’yan sanda, wanda shi ma ya yi hadaya da awaki 26, don girmama shugabansa. Daga bisani, minister ya shirya bikin cin abinci ga magoya bayansa, don murnar ci gaban da ya samu.
“Ina da imani sosai da abin bauta, amma yanzu imanina ya karu lokacin da burina ya cika,” a cewar ministan, kamar yadda ya bayyana wa manema labarai. Wannan dakin bauta yana can a kan wani tsauni da ke kewaye da korayen furanni a gandun daji.
Masu fafutikar kare hakkin dabbobi sun soki lamirin ministan da kakkausar murya, inda suka ce wannan abin bakin ciki jin cewa shugaban al’umma ya yanka awakai, don kawai ya faranta wa abubuwan bautarsa, bayan bukatarsa ta biya. Sun ce ministan bas hi d amasaniya kan dokar da ta haramta keta haddin dabbobi, ta shekarar 1960, wadda ta haramta yanka dabbobi a fili, a lokutan bukukuwan addini.
“daukacin addinai na karfafa muhimmancin tausasawa, don haka akwai hanyoyin sadaukarwa ba tare da an nuna son rai ba, ta hanyar daukar rai, tunda ana iya raba abinci ga masu cin ganyayyaki da tufafi ga matalauta. Idan masu yawon shakatawa suka samu labarin keta haddin dabbobi da ministan ya yi wa dabbobi, to za su fasa yin ziyarsu a Jharkhand,” a Bhubaneshwari Gupta, Babban Jami’in kungiyar Masu Fafutikar Kare Hakkin Dabbobi ta PETA,  kamar yadda yake kunshe a sakon i-mail da ya aike wa Jaridar Gulfnews daga birnin Mumbai.

Ban zama Shugaban Kasa don na tara kuɗi ba — Tinubu

Babu buƙatar mu riƙa tsayar da motoci muna duba takardu — ’Yan sanda

‘Yan bindiga sun ƙone gidan mai da motoci 4 a Enugu

Kwalara ta kashe fiye da mutum 300 a Sudan